Shugaban Mabiya Darikar Cocin Katolika na Duniya, Pope Francis yace bai kamata ana tozarta duk wata macen da ta zubar da ci ba.
Ya ce kamata ya yi a nemi hanyar kwantar mata da hankaline ganin cewa ba abu mai sauki bane mace ta zubar da cikin dake jikinta.
Pope Francis ya fadi haka ne ranar Litini da ya ke zantawa da manema labarai bayan ya dawo ziyara da ya kai kasar Panama.
Ya ce a ra’ayinsa bai kamata ana tozarta mace ba saboda ta zubar da ciki, maimakon haka jawo ta a jiki za ayi sannan a kwadaitar da ita mahimmancin nemi gafarar bisa abinda da ta aikata.
‘‘Kamata ya yi mutane su gane cewa Allah na yafe wa ‘ya’yan sa zunuban su musamman idan suka yi tuba na gaskiya.
‘‘Amma tozata mace saboda cire ciki baya maganin komai illa ya kara jefa ta cikin matsaloli.
Yayin da Pope Francis yake Kasar Panama ya yi adu’a Allah ya ganar da kasashen duniyan da suka kafa dokar hana cire ciki a kasashen su.
Duk da haka Pope Francis ya ce yana nan akan bakan sa na nuna ki ga amfani da dabarun bada tazarar iyali.
” A ra’ayi na cire ciki kamar ka nemi taimakon wani ya kawar maka da matsalar da kake fama da shi kawai.”