ZAZZABIN LASSA: Mutane bakwai sun rasu a jihohin Ebonyi da Filato

0

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Ebonyi Daniel Umezuruike ya bayyana cewa zazzabin lasa ya kashe mutane biyu a jihar.

Umezuruike ya fadi haka ne da yake gana wa da manema labarai a garin Abakaliki.

Ya ce an rasa rayukan wadannan mutane biyu ne a asibitin kula da masu fama da zazzabin lasa dake Abakaliki.

Bayan haka kwamishinan kiwon lafiya na jihar Filato Kunden Deyin ya bayyana cewa mutane 17 sun kamu da zazzabin lasa a jihar.

Deyin ya ce an gano haka ne bayan gwaji daaka yi wa. Saidai cikin su mutane 5 sun riga mu gidan gaskiya.

”A yanzu haka mutane 13 na samun sauki a asibiti sannan saura kuwa an sallame su.

”Mun kebe mutane 73 wadanda muke zaton sun yi mu’amula da mutane 17 din dake dauke da cutar sannan za a sallame su da zaran an tabbatar basa kamu da cutar.

Kwamishinonin sun yi kira ga mutane da su gaggauta garzayawa asibiti da zaran basu dadi a jikin su ba.

Sun kuma bayyana wasu hanyoyin da mutane za su iya bi domin gujewa kamuwa da cutar.

Ga hanyoyin

1. Da zaran mutum ya kamu da zazzabi a tuntubi likita domin tabbatar da cutar da mutum ke dauke da shi.

2. Duk ma’aikacin kiwon lafiya da zai duba mara lafiya a asibiti ya tabbata yana sanye da safar hannu sannnan ya kuma tabbata ya wanke hannayen sa da kyau bayan ya gama duba mara lafiya.

3. Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbatar sun nemi magani da zarar alluran da suka yi amfani da shi a jikin wanda ke dauke da cutar ya soke su.

4. A tabbata an tsaftace muhalli da kuma adana kayan abinci neasa da fitsari da kuma kashin beraye.

5. Ba a iya kamuwa da cutar zazzabin Lassa idan an taba wanda ke dauke da cutar amma za a iya kamuwa da shi idan yawu, jini ko kuma zufan wanda ke dauke da cutar ya taba wanda ba ya da shi.

Share.

game da Author