Da ina da guntun kashi da gwamnati ta tsoma ni cikin ruwan zafi -Saraki

0

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya ce da akwai wani laifin harkalla tare da shi, to da tuni gwamnatin tarayya ta ga bayan sa.

Haka ya bayyana a wani taron liyafa da aka shirya masa a Karamar Hukumar Offa, jihar Kwara, a lokacin da ya je kamfen.

Saraki wanda a wurin ya yi wa jiga-jigan PDP na yankin jawabi, ya kara jaddada musu cewa gwamnatin Buhari ba ta da wani tanadi kuma ba za ta yi wani tanadi don ci gaba al’ummar jihar Kwara ba.

Kakakin yada labarai na Saraki a fannin soshiyal midiya, Olu Onemola ne ya bayyana faruwar wannan taron.

Saraki ya ci gaba da cewa ya na fitowa gaba-gadi ne ya na kalubalantar gwamnatin Buhari, saboda ya san ba shi da wani guntun kashi a gindi.

Sai ya kara da cewa da ya na da kashi a gindi, to da tuni gwamnati ta tsoma shi a ruwan zafi, ya yi tsamo-tsamo.

“Duk mai kaunar ci gaban Jihar Kwara to ba zai bi guguwar Buhariyya a wannan zaben ba. Domin Buhari bai yi wa Kwara wani tanadi karami ko mai girma ba.

“Jiga-jigan APC ‘yan asalin jihar Kwara ba su da kimar da za su iya tunkarar Buhari da wasu bukatun su ko karafin su. Wai sai dai su rika daukar rubutacciyar takarda su kai wa wani gogarma can da ke Lagos, shi kuma ya kai masa.”

Saraki ya karkare da cewa kada a kuskura a zabi PDP, domin a nuna wa cewa Jihar Kwara ta fi karfin wani kokirzo ya rika mulkar ta daga Lagos.

Share.

game da Author