Dalilan da suka sa na dakatar da Babban Mai Shari’a, Onnoghen – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana dalilan da ya ce su ne suka sa ya dakatar da Babban Mai Shari’a na Kasa, Cif Walter Onoghen.

Buhari ya bada dalilan ne biyo bayan odar da ya samu daga Kotun CCT na ya gaggauta dakatar da Alkalin Alkalan Najeriya din.

An maye gurbin sa da Tanko Mohammed wanda aka rantsar da yammacin ranar Juma’a.

A cikin wani jawabi da ya fitar a yau, Buhari ya kafa hujjoji ne da zargin kin bayyana kadarorin sa da ake yi masa a gaban Kotun CCT.

1 – Na dakatar da shi ne bisa dalilin odar da Kotun CCT ta ba ni cewa na gaggauta dakatar da shi, saboda ya na fuskantar tuhumar kin bayyana kadadorin sa.

2 – Tuhumar da ake yi masa mai karfi ce kwarai. Sai kuma aka sake gano cewa akwai wasu milyoyin kudade da ya mallaka, wadanda su ma ko dai bai bayyana su ba, ko kuma ya yi ‘yar-burum-burum wajen bayyana hakikanin adadin sa.

3 – Bugu da kari kuma sji da kan sa ya rubuta wa kotun CCT cewa kuskure ne ya yi da bai bayyana kadarorin ba, da kuma hali na mantuwa. Wadannan kuwa shi Onneghan ya san ba abin laminta ba ne a shari’a.

4 – Abin da kowa zai yi tunani daga Onneghan shi ne tun da dai shi da kan sa ya rattaba cewa ya yi kuskure da kuma mantuwa, to kamata ya yi kawai ya yi wa kansa adalci ya sauka ya bari sai an ga yadda shari’a ta kaya tukunna.

5 – Maimakon ya sauka ya bari a yi shari’a, sai ya zauna ya bar kasan nan ta shiga karankatakaliya, kowa na fadin ta-sa-ta-fishse-shi.

6 – Onnoghen da zugar lauyoyin sa suka rika tozarta kotun CCT, maimakon su fara barin ta saurari zargin da ake yi masa tukunna.

7 – Ko ma ta wace fuska mutum zai yi tunani, karfi da mauyin mukamin da Onnoghen ke rike za a kalla a matsayin sa na Babban Alkalin Najeriya gaba daya.

8 – Tun daga ranar da aka fara batun shari’ar Onnoghen, sai kotuna suka rika tseren bada odar soke hukuncin waccan kotun duk a kan batun na Alkalin Alkalai.

9 – Wadannan umarni da kotuna suka rika bayar wa, sun samu goyon baya daga alkalai masu kallon ko daidai ko ba daidai ba ne, to hakan daidai ne. Alhali kuma kotu.

10 – A fili ta ke cewa wannan gwamnatin ba gaba gamsuwa da yadda Kotun Koli a karkashin Walter Onnoghen ke sallamar karrakin wadanda ake zargi da rashawa haka kawai a bisa kawo wasu hujjojin da za a rika cewa shari’a-sabanin-hankali.

Share.

game da Author