Masu yi wa EFCC zanga-zanga sun nemi ta gurfanar da Akpabio

0

Jiya Litinin ne masu zanga-zanga suka yi dafifi a ofishin EFCC da ke Wuse 2, Abuja, inda suka nemi a binciki tsohon gwamnan Jihar Akwa-Ibom, Godswill Akpabio.

Masu zanga-zangar sun fito ne a karkashin wata kungiya mai suna ‘Civil Society Group for Accountability and Probilty’, sun nemi a binciki Akpabio a kan mallakar manyan kadarori da kuma yin rantsuwar karya wajen bayyana kadarorin sa, a matsayin san a sanata.

Kakakin masu zanga-zangar, Jonathan Ogwuche, ya ce sun je EFCC ne domin su bayar da takardar korafi a kan Akpabio.

Sun ce a cikin 2007, Akpabio ya ce ya na da gidaje 8, a cikin 2011 ya ce ya na da 11.”

“Abin mamaki, kuma abin damuwa, cikin 2016, rahotanni a cikin wata jaridar online ta ce ya mallaki gidaje a Dubai.

1. Plot 5 Ikogosi Spring Close, Maitama-Abuja;
2. Plot 28 Colorado Close, Maitama;
3. 22 Probyn Road, Ikoyi, Lagos;
4. Plot 23 Olusegun Aina Street, Parkview, Lagos.”

Masu zanga-zangar sun bayyana wa EFCC a rubuce cewa Akpabio bai saka sunayen wadannan maka-makan gidajen a cikin rantsuwar bayyana kadarorin sa ba.

Sun kuma yi maganar cewa ya na da wasu bargar motocin da bai bayyana cewa ya mallake su ba.

Kakakin yada labarai na Akpabio, Anietie Ekpong, ya ce wa PREMIUM TIMES ba su yi mamakin wadannan zarge-zargen da aka yi wa Akpabio ba.

Ya ce ba sau daya ba, sun sha zuwa ofishin EFCC Akpabio na yin jawabi a kan wasu korafe-korafe da aka kai a kan sa.

Ya ce duk sharrin masu adawar siyasa ne kawai, ba gaskiya ba ne.

AKPABIO: MAI HANNU DA SHUNI AKE BA MURJIN ZARE
An zabi Akpabio a matsayin gwamnan Akwa-Ibom cikin 2007. Ya kammala wa’adin sa cikin 2015, duk a karkashin PDP. Ya ci takarar Sanata a 2015 karkashin PDP.

A lokacin da ya na gwamna an rika tura wa jihohi makudan kudade, musamman masu arzikin danyen man fetur.

Jihohin Akwa-Ibom da Rivers ne johohi mafi karfin arzkin danyen man fetur, Kuma su ne jihohin da suka fi karbar makudan biliyoyin kudade daga asusun gwamnatin tarayya.

Bayanai daga Hukumar Kididdiga sun tabbatar da nuna cewa Akwa-Ibom ta karbi jimillar naira tiriliyan 1.6 tsakanin Yuni, 2007 zuwa Mayu 2014, a lokacin mulkin Akpabio kenan.

Cikin watan Agusta, 2018 ya fice daga PDP ya koma APC.

Ana zargin ya wawuri naira biliyan 112, kuma tun bayan komawar sa APC ba a sake jin inda zance ya kwana ba.

Share.

game da Author