Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa daya daga cikin dalilan da ya sa manyan mutane a jihar Kaduna suka ki jinin sa shine kawai don ya ce ba zai yi watanda da kudaden jihar ba , aiki za ayi wa talakawa.
El-Rufai ya fadi haka ne a hira da yayi a gidan radiyon tarayya na Kaduna FRCN, a ranar Asabar.
El- Rufai ya ce tun bayan hawan sa mulki ya soke raba wa manya dake zaune haka kawai sai da arika tura musu kudaden talakawa kyauta, maimakon haka gwamnatin mu ta ce a’a ba za ayi haka ba, makarantun da talakawa ke tura ‘ya’yan su, da asibitoci za a maida hankali wajen gyarawa.
” Za mu rugurguza wannan katangar da ke tsakanin masu wadata wato wadanda suke ganin su ne manya a jihar da talakawa wajen ganin mun karkata kacokan zuwa ga samar wa talakawan Kaduna ababen more rayuwa da suka hada da samar da makarantu da magartattun malamai, kiwon lafiya da inganta jihar.
” A haka muke ganin cewa talakawa da mutanen Kaduna sun amince da mu da abinda muka sa a gaba sannan muna da yakinin suna tare da mu zasu mara mana baya mu kai ga nasara a zabukan masu zuwa.
” Idan mutum bashi da lafiya rangaranga aka garzaya da shi asibiti, ba addini ko kabilar likitan yake tambaya ba, abinda ke gaban sa a lokacin shine kawai yadda zai samu lafiya, haka idan ya hau jirgi ko kuma ci gaban sana’arsa, duk wadanda suka kware ake nema amma idan yazo ga gwamnati sai a sako banbance-banbance na addini ko kabilaci a ciki.
” Wannan shine babban dalilin da ya sa muka zabi kwararriya, wato, Hadiza Balarabe domin zama mataimakiya ta. Dacewa da kwarewa domin ci gaban Kaduna ne ya sa muka yi wannan zabi ba tare da addini ba ko kabilar da ta fito.
Discussion about this post