ZARGIN KAZAFI: Magu ya gabatar wa kotu shaidar mallakar gida daya a Abuja

0

Jiya Alhamis ne Shugaban Riko na Hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya gabatar da shaida a kotu, dangane da abin da ya kira kazafin da ya ce jaridar The Sun ta yi masa, na mallakar gidaje biyu a Abuja.

An fara tafka wannan shari’a dai a gaban alkalin Babbar Kotun Lagos, da ke Ikeja.

Magu ya musanta cewa shi da matar sa su na da gidaje biyu a Abuja, inda ya jajirce cewa guda daya tal suka mallaka.

Jaridar The Sun ce dai ta taba buga wani labari inda ta ruwaito cewa ta gano wasu gidaje biyu da Magu ya mallaka, masu dauke da sunan mallakar matar Magu din.

Shugaban na EFCC ya kuma shaida wa kotu cewa rahoton da THE SUN ta ci gaba da bayarwa cewa hukumar SSS na yi wa Magu matsanancin bincike, karya ce, ba gaskiya ba ce.

“Ni fa tun da na zo EFCC babu wanda ya taba bincike na.” Inji Magu.

Idan ba a manta ba, cikin 2017, EFCC sun kutsa cikin hedikwatar jaridar THE SUN a Lagos, inda suka bada dalilin cewa sun je ne domin zagayen gani-da-ido na ilahirin kadarorin da ke cikin kamfanin, domin bin diddigin batun umarnin da kotu ta bayar tun 2007, cewa EFCC ta kwace kamfanin ta rike a hannun ta, kafin har lokacin da shari’ar da ake yi da shugaban kamfanin, Orji Uzor Kalu ta kaya.

Sai dai kuma jaridar ta yi watsi da ikirarin dalilin shigar kutsen da EFCC ta yi a 2017, inda ta ce karya hukumar ke yi, EFCC ta je ne saboda binciken da jaridar ke yi na wasu gidaje da ta ce matar Shugaban EFCC Magu ta mallaka.

Kwanaki kadan bayan buga labarin da kuma kai farmakin a ofishin The Sun, sai Magu ya maka jaridar kara, kuma ya nemi a biya shi diyyar naira milyan 100 saboda bata sunan sa da jaridar ta yi.

Ya kuma nemi jaridar ta buga ban-hakuri tare da karyata kanta da kanta, cewa labarin da ta buga ba gaskiya ba ce.

Magu ya nemi jaridar ta rika buga labarin karyata kan ta da ba shi hakuri, har tsawon kwani bakwai a jere, ba tare da tsallaken ko da kwana daya ba.

Tun a ranar 25 Ga Maris, 2017, Magu ya bayyana cewa:

“Ta ina zan iya zuwa na sayi gida a Maitama? Mata ta kuma ma’aikaciyar gwamnati ce. Gida daya kawai muka mallaka, shi ma mun dade da sayen sa, can a Karu, ba cikin birnin Abuja ba.

Magu ya bayyana wa kotu cewa wani karin abin haushi, jaridar THE SUN har garin su ta je ta na binciken sa.

A kotun an tambayi Magu shin ko dai ita ma jaridar ta kwaso wani rahoto ne daga wata hukumar da ke binciken sa? Sai ya ce ba haka ba ne, shi babu wata hukuma da ke binciken sa.

Ya kara shaida wa kotu cewa inda ma rahoton na jaridar ke da rauni, ba ta fadi wuraren da ta ce gidajen na shi Magu din da matar sa suke ba.

Da aka tambaye shi batun kin tantance shi da Majalisar Dattawa ba ta yi ba, sai ya ce shi ya gode wa Allah da Majalisar Dattawa ba ta tantance shi ba.

Ya ce da ta tantance shi, to da yanzu ba zai iya yin aikin sa kamar yadda ya ke yi a yanzu ba.

Share.

game da Author