Wani mai bayar da shaida a shari’ar da Shugaban Gidan Talbijin na AIT, Raymond Dokpesi ya maka Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed, ya bayyana wa Babbar Kotun Abuja abin da ya ce ya ji da kunnen sa da kuma wanda ya gani da ido ya karanta, na game da kalaman batanci da Lai ya yi wa Dokpesi.
Linan Okpanu, ya je kotu ne domon bayar da shaidar zargin bata suna da Dokpesi yay i ikirarin cewa Lai Mohammed yayi masa.
Dokpesi ya shigar da kara tun cikin watan Afrilu, ya na neman diyyar naira bilyan 5 daga hannun Ministan Yada Labarai Lai Mohammed da kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, saboda bata masa suna da ya ce an yi.
Ya ce Mohammed da Malami sun bata masa suna, saboda sun tsoma sunan sa a cikin wadanda Lai ya bayyana cewa sun wawuce dukiyar kasar nan.
Da ya ke bada shaida, Okpanu, ya ce ya ji da kunnen sa kuma ya gani a gidan talbijin na Channels, lokacin da ake hira da Lai, ya ambaci sunan Raymond Dokpesi.
Kuma y ce baya da nan ma, ya gani a kafar soshiyal midiya ta ‘Youtube’.
Okpanu, wanda mazauni Ingila ne, ya shaida wa kotu cewa: “Da kunne na na ji Ministan Yada Labarai ya kira sunan Dokpesi, a cikin wadanda ke takardar mai kunshe da sunayen da Lai din ya ce su ne suka kassara kasar nan.
Baya ga Okpanu, wasu masu gabatar da shaidu uku duk sun bayar inda suka nuna wa kotu cewa ran su ya sosu a matsayin su na abokai da abokan huldar Dokpesi, jin cewa an bayyana shi a matsayin wanda ya wawuri dukiyar Najeriya.
Mai shari’a ya dage sauraron karar zuwa ranar 27 Ga Fabrairu, 2019.
Baya ga neman diyya da Dokpesi ke yi ta naira biliyan 5, ya na kuma neman kotu ta tilasta Lai ya buga bayanin janye sunan Dokpesi daga wadanda suka wawuri dukiyar kasar nan.
Sannan kuma ya na son kotu ta tilasta ministan buga wasikar bada hakuri a wasu manyan jaridun kasar nan da gidajen radiyo da talbijin.
Ya kuma nemi kotu ta gargadi ministocin biyu ko wasu ko wani ejan na gwamnati kada su kara bata masa suna.