Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa gwamnatin sa ba za ta nade hannu ta zuba wa wadanda suka tada rudadnin da ya auku a Kasuwar Magani ba.
El-Rufai ya ce duk wanda bincike ya bayyana yana da hannu a wannan rikici zai dandana kudan sa domin gwamnati za ta hukunta shi kamar yadda doka ya gindaya.
Idan ba a manta ba Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Kaduna, ya bayyana cewa an kashe mutane 55 a kazamin rikicin da aka yi a watan Oktoba, a garin Kasuwan Magani, cikin Karamar Hukumar Kajuru, a jihar Kaduna.
Kwamishina Ahmed Abdur-Rahman ya bayyana haka ne da yake zantawa da manema labarai a Kaduna,sanna kuma ya ce ‘yan sanda sun kama mutane 22 da ake zargi da hannu a wannan tashin-tashina.
El-Rufai ya bayyana haka ne a taron da yayi da mutanen garin Kasuwar Magani da kewaye inda ya shaida musu cewa lallai gwamnati za ta hukunta duk wanda ta samu da laifi a wannan rikici.
Hakimin Kufana, Titus Dauda ya bada shawarar a karo jami’an tsaro a wannan yanki cewa hakanne kawai zai kawo karshen irin wannan tashin hankali da ake fama dashi a wannan yanki.
Suko kungiyoyin addinai na Musulmai da Kirista shawarar su daya ne cewa idan ba hukunta wadanda suke tada irin wannan tashin-tashina ake yi ba ba za a taba samun zaman lafiya ba. Sun kara da cewa gwamnati ta rika hukunta masu tada irin wannan rikici cikin gaggawa shine mafita.
Discussion about this post