Uwargidan mataimakin shugaban kasa Dolapo Osinbajo ta bayyana cewa kungiyar ta na yaki da amfani da miyagun kwayoyi za ta mara wa kokarin da gwamnati ke yi wajen ganin an hana matasa ta’ammali da miyagun kwayoyi a kasar nan.
Dolapo ta fadi haka ne ranar Talata yayin da ta kai wa ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ziyara a Abuja.
Ta bayyana cewa inganta hanyoyin hana amfani da miyagun kwayoyi na da matukar mahimmanci ganin cewa matsalar ta ki ci ta ki cinyewa a kasar nan.
Dolapo ta ce kwanakin baya gwamnati ta hana shigowa da sarrafa maganin tari na kodin amma haka ya haifar da sauran miyagun kwayoyi ne da suke a boye yin tasiri.
” Za kuma mu tabbatar cewa asibitocin kula da masu yin ta’ammali da miyagun kwayoyi na na yi musu khuduba ta gari wanda zai amfanar dasu da hana su ci gaba da shan irin wadannan kwayoyi.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne shugaban kungiyar gwamnonin matan Arewa kuma uwargidan gwamnan jihar Bauchi Hadiza Abubakar ta bayyana cewa shaye-shayen miyagun kwayoyi ya zama ruwan dare a yankin Arewa sannan ya lalata rayuwar matasan yankin da idan ba ayi wani abu cikin gaggawa ba za a fada cikin matsanancin hali a yankin.
Bayan haka Hadiza ta ce sun yanke shawara cewa kowace matan gwamna a kasar nan za ta bude wuri don horas da wadanda suka fada cikin wannan matsanancin hali da nufin ceto rayuwar su.
” Za kuma mu ci gaba da hada hannu da masu ruwa da tsaki na Arewa domin ganin mun kawo karshe wannan mummunar matsalar a yankin.”