Za a yi jana’zar marigayi Shehu Shagari a garin Sokoto

0

Kamar yadda ‘Yan uwan marigayin suka sanar, za a yi jana’zan tsohon shugaban kasa Shehu Shagari ranar Asabar a garin Sokoto.

Shehu Shagari ya rasu a babban asibitin gwamnatin tarayya da ke Abuja, wato National Hospital bayan ‘Yar gajeruwar rashin lafiya da yayi fama da shi.

Shehu Shagari ya shugabanci Najeriya daga 1979 zuwa 1984, bayan an yi wa gwamnatin sa a wancan lokaci juyin mulki.

Jikan marigayin Bello Shagari da gwamnan jihar Sokoto ne suka sanar da rasuwar marigayi Shehi Shagari.

Share.

game da Author