Hukumar Kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na kasa (NPHCDA) ta bayyana cewa za ta horas da wasu ma’aikatan ta 30 domin inganta aiyukkan da take yi a kasar nan.
Shugaban hukumar Faisal Shu’aib ya sanar da haka a taron horas da ma’aikatan da aka yi a Abuja.
Ya ce NPHCDA ta sami goyan bayan kungiyar Solina Health da gidauniyyar Bill da Melinda Gates domin horas da wadannan ma’aikata da suka zaba.
Daya daga cikin ma’aikatan da aka zaba din mai suna Olalekan Oladele ta jinjina wa hukumar NPHCDA tana mai cewa horan da za su samu zai taimaka wa ma’aikatan hukumar wajen gudanar da shiri da kudirorin inganta fannin kiwon lafiyar mutanen kasar nan.
Idan ba a manta ba a shekaran 1992 ne gwamnati ta kafa hukumar NPHCDA domin inganta kiwon lafiyar da mutane musamman mazaunan karkara ke samu a cibiyoyin kiwon lafiya.
Bincike ya nuna cewa cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko 30,000 ne ake da su a kasar nan inda daga cikin kashi 20 bisa 100 ne kadai ke aiki yadda ya kamata.