Kakakin hukumar kashe gobara na jihar Kano Saidu Mohammed ya bayyana cewa sun tsamo gawar wani yaro a kogin Mariri Yankatsari dake karamar hukumar Dawakin Kudu.
Mohammed ya fadi haka ne da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Laraba.
Ya ce ma’aikatan hukumar sun iske gawar Dayyabu Salisu yana yawo a kogin bayan wani Malam Saminu Sani ya kira su da karfe 10:43 na safe.
” Mun sami labarin cewa Dayyabu mai shekaru 13 ya je wannan kogi ne don ya yi wanka.
Mohammed ya yi kira ga iyaye da su rika kula da shige da ficen ‘ya’yan su domin gudun haka.
Discussion about this post