Dandazon jami’an ‘yan sanda sun rufe kofar shiga Majalisar Tarayya, inda suka hana ma’aikatan majalisar da sauran jama shiga ciki.
’Yan sanda, wadanda suka yi cirko-cirko ta bangaren kofar da ake shiga daga Gidan Gwamnatin Tarayya, sun rika maido duk ma wanda ya tunkari shiga ciki baya.
Sun hana shiga ne, bayan da shugabannin majalisar sun nemi jami’an tsaro na SSS da ‘yan sanda su bayar da tsaro ga majalisar domin ta gudanar da zaman ta na yau Talata.
Rikita-rikita ta taso bayan da kungiyar ma’aikatan majalisar tarayya suka fara gudanar da zanga-zanga jiya Litinin, har suka hana ma’aikatan majalisar gudanar da aikin su.
Su na nuna bacin ran su ne saboda abin da suka kira yadda ake rikon-sakainar-kashi da hakkokin su da kuma rashin kulawar yadda ta kamata da ba a yi musu domin gudanar da aikin su.
Dama ko cikin makonni biyu da suka gabata sai da ma’aikatan suka gudnar da zanga-zanga a cikin harabar majalisar.
Sun gudanar da zanga-zanga jiya Litinin bayan sun bayar da gargadin kwanaki hudu na a biya su hakkokin su ko su fara zanga-zanga.
Idan suka ci gaba da wannan zanga-zanga, hakan zai iya shafar zuwan Shugaba Muhammadu Buhari a gobe Laraba domin ya gabatar da kasafin kudi na 2019.
Discussion about this post