Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta bayyana cewa daga cikin ‘yan sandan da aka aika jihar Zamfara domin fatattakar maharan da suka hana mutanen jihar sukuni 16 kawai suka rasu.
Rundunar ta sanar da haka ne ranar Talata da yamma inda ta kara da cewa rundunar ta kuma gano wasu ‘yan sanda 20 da suka bace yayin da suke aiki.
” A dalilin haka muke sanar da cewa za mu karfafa tsaro domin ganin mun taso keyar duk wani mahari dake yankin arewa maso yammacin kasar nan.
Wannan sanarwa da rundunar ta yi ya sha bam-bam da sanarwar kashe mahara 104 da ‘yan sandan suka yi a karamar hukumar Zurmi.
Bisa ga sanarwar rundunar ta rasa dan sanda daya ne kadai sannan ta ragargaza maboyar mahara 50 tare da kwato shannu da tumakai da dama.
Sai dai kuma a ranar 2 ga watan Nuwamba wata majiya daga rundunar ‘yan sandan ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa a dalilin arangamar da ‘yan sanda da mahara suka yi a karamar hukumar Zurmi rundunar ta rasa ‘yan sanda 50.
Majiyar ta kuma kara da cewa har yanzu rundunar bata iya kwaso gawarwakin wadannan ‘yan sanda da aka rasa ba.
Bayan gidan jaridar ta wallafa wannan labari ne dan takaran shugaban kasa daga inuwar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya yi kira ga gwamnati don kebe ranaku akalla bakwai domin yin juyayin mutuwar ‘yan sanda da sojojin da aka rasa a a Barno.
Bayanai sun nuna cewa rundunar ‘yan sandan ta bada wannan sanarwa ne domin kwantar da hankulan ‘yan uwan ‘yan sandan da suke barazanar daukan mataki idan har rundunar ta ci gaba da yin kunen uwar shegu da su game da labarin ‘yan uwan su.
” Tun da PREMIUM TIMES ta wallafa labarin cewa mahara sun kashe ‘yan sanda 50 a jihar Zamfara muke neman karin bayanin daga wajen hukumar game da ‘yan uwan mu da suke aiki a jihar ammasuka ki waiwayar mu.
A yanzu dai rundunar ta ce za a birne duk ‘yan sandan da suka rasa sannan za su tabbatar cewa sun biya iyalen wadanda aka rasa kudaden diyya rai da ‘yan uwan su.
A yankin Zurmi da kewaye, akwai dimbin makiyaya da manoma, wadanda ke fuskantar hare-hare, kisa, kona dukiyoyi da kuma garkuwa daga masu kai musu hare-hare.
Ya zuwa watan Agusta, 2018, an kiyasta kashe mutane 3,000 a yankin Zamfara, kamar yadda gwamnatin jihar ta fitar da sanarwa.
Dubbai kuma sun gudu neman mafakar gudun hijira a kauyuka da garuruwa da dama.
A kokarin da ‘yan sanda ke yi na dakile masu hari da garkuwa da satar shanu a Zamfara, sun yi kira da cewa duk mai wani labarin inda mahara suke, ko yin wani karin haske, to zai iya kiran wadannan lambobin:
08037025670, 08033210966, 08033312261, 08123829666, 09053872244, 07082351758 and 08091914752.
Discussion about this post