‘Yan Majalisar da suka ci wa Buhari mutunci sakarkarun ’yan siyasa ne – Kungiyar MURIC

0

Kungiyar Kare Hakkin Musulmi da ake kira MURIC, ta kira ‘yan majalisar da suka yi wa Shugaba Muhammadu Buhari eho da sowa a lokacin da ya ke gabatar da kasafin kudi, cewa shashashu, sakarkaru kuma dolayen ‘yan siyasa ne
Wannan kakkausan furuci da MURIC ta yi, ya na kunshe ne a cikin wata doguwar takardar jawabi da ta aiko wa PREMIUM TIMES.

Shugaban Kungiyar wanda farfaesa ne, Ishaq Akintola, ya ce dabi’ar ‘yan siyasar yaranta ce, jagaliyanci ne kuma kidahumanci a cikin abin na su.

Akintola ya ce abin da ‘yan majalisar suka yi wa Shugaba Buhari, ya nuna akwai yaranta da rashin sanin ya kamata a zukatan su, kuma ya nuna yadda suka zubar da kimar majalisar.

Ya kara da cewa abin da ya faru a lokacin da Buhari ke gabatar da jawabin sa, ya zama shaidar kukan da jama’a ke yi a baya cewa wannan majalisa da ke kan mulki yanzu, cike ta ke makil da ‘yan barababiya, ‘yan ragabza, ‘yan bulkara da harmagaza, wadanda ba su san alkiblar da ta dace su bi ba.

“A rika yi wa shugaba eho da sowa ba kakkautawa a lokacin da ya ke karanta kasafin kudi, ya nuna wadannan ‘yan majalisa ba su kaunar ci gaban kasar nan.

“MURIC ba ta na adawa da ‘yan majalisa ba ne don sun yi adawa da shugaban kasa. Amma a ci gaba da sowa har ta wuce gona da iri ba tare da an tsaya ba, wannan ba karamin sakarci ba ne.”

MURIC ta kuma nuna bacin rai yadda sowar da aka rika yi har ta sa Kakakin Majalisar Tarayya Yakubu Dogara bai samu damar karatan jawabin rufe taron ba. Ya ce wannan abin takaici ne kwarai.

Daga nan sai ya tunatar da yadda su ‘yan majalisar suka jefa kasar nan cikin alakakai a baya lokacin da suka rike kasafin kudi wa yi wata da watanni ba tare da sun sake shi ga shugaban kasa ya fara gudanar da ayyukan raya kasa da wuri ba.

Share.

game da Author