‘Yan majalisa sun tada da tarzoma da niyyar tozarta Buhari idan ya zo gabatar da Kasafin kudi

0

Wasu daga cikin’yan majalisar tarayya sun tada balli a majalisa dauke da kwalaye domin yin zanga-zangar nuna fushin su ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A yau Laraba ne shugaba Buhari zai gabatar da kasafin kudi na 2019 a zauren majalisar. Sai dai hakan ya zo da tangarda domin kuwa wasu daga cikin yan majalisar sun ja daga cewa sai sun murza masa rashin mutunci idan yazo.

A haka ne dai wasu daga cikin magoya bayan Buhari a majlisar, kamar su Honorabul Gudaji Kazaure inda ya bi ‘yan majalisar ya rika kwace takardun da suke dauke da su a hannayen su

Zuwa yanzu dai zaman lafiya ya dawo sannan ‘yan majalisar sun koma domin ci gaba da yin muhawarar yadda za su karbi shugaba Buhari a majalisar.

A haka kuma wani dan majalisar dake zauren majalisar ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa shi da kansa ya hangu Kakakin majalisar wakilai ya durkusa yana rokon hasalallun ‘yan majalisar da kada su tozarta Buhari idan ya zo majalisar.

Share.

game da Author