YAJIN AIKI: Sake zaman sulhun gwamnati da malaman jami’o’i bai yi tasiri ba

0

Wani taron neman sasantawa da gudanar jiya Talata tsakanin gwamnatinn tarayya da Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya, ASUU, bai yi nasara ba, saboda ba a samu sasanta janye yajin aikin da malaman ke yi tun farkon watan Nuwamba ba.

An gudanar da taron a Ma’aikatar Kula da Harkokin Ilimi, Abuja. Wannan taro shi ne na biyu tun bayan da malaman suka shiga yajin aiki.

Tun ranar 4 Ga Nuwamba ne malaman suka shiga yajin aiki, saboda fushin su kan gwamnatin tarayya ganin yadda kamar yadda suka yi ikirari, ta na yawan daukar musu alkawarin biyan bukatun su, amma ba ta cikawa.

Bayan tashi daga taron jiya Talata, Shugaban ASUU, Biodun Ogunyemi, ya shaida wa manema labarai cewa har yau bangarorin biyu ba su cimma matsayar da har za su iya amincewa su janye yajin aikin da suke yi ba.

Ministan Harkokin Ilmi, Adamu Adamu, Babban Sakataren Ilmi na Kasa, Sunny Echono da kuma wakilan Hukumar Kula da Jami’o’i da na Hukumar Kula da Kudaden Shiga da Tsara Albashi ta Kasa.

A gefe daya kuma Shugaban Kungiyar Dalibai ta Kasa (NANS), Dalibai ya yi kiran bangarorin biyu su sasanta, kuma jikan dalibai, wadanda su ne wannan yajin aikin ke fuskanta.

Share.

game da Author