Kungiyar Daliban Jami’o’i ta Najeriya (NANS), ta fitar da sanarwar bada wa’adin mako biyu ga gwamnatin tarayya da kuma Kungiyar Malaman Jami’o’i da su sasanta a janye yajin aiki, ko kuma su shirya yin fito-na-fito.
Wannan kakkausan furucin ya na kunshe ne a cikin takardar da Shugaban Kungiyar Daliban Jami’a na Kasa, Daniel Akpan ya fitar ranar Lahadi.
ASUU ta fara yajin aiki tun daga ranar 4 Ga Nuwamba, bayan ta zargi gwamnatin tarayya da kin cika mata tsoffi da sabbin alkawurran da ta dauka.
Daga ranar da malaman jami’a suka fara yajin aiki zuwa makon da ya gabata, an yi zaman sulhu sau bakwai tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman, amma a ko da yaushe ana watsewa baram-baram.
Cikin makon da ya gabata ne ASSU ta ce ta daina zama da gwamnatin tarayya, domin ta lura gwamnatin mayaudara ce kawai.
Kungiyar daliban ta kuma soki lamirin yadda ita kungiyar malamai ba ta so wakilan kungiyar dalibai ta zama ‘yar kallo a lokacin zaman sasantawa tsakanin malamai da gwamnati.
Akpan ya ce wannan yajin aiki da ake yi ya shafi karatun su, ya kuma shafi rayuwar su, kuma zai kawo musu cikas wajen subucewar damar su ta yin zaben 2019.
Akpan ya ce daliban jami’o’i sun damu kwarai da yadda gwamnati da kuma malaman jami’a ba su tausaya musu, kuma su na nuna ba su damu da makomar karatun su ba.
A karshe ya yi barazanar cewa daliban jami’o’i za su fito su yi zanga-zanga a fadin kasar nan, tare da yin gangamin dalibai 100, 000 da ya ce za su shigo su yi hayaniya a Abuja, babban birnin tarayya.