WATA SABUWA: Dalilan da ya sa Buhari zai iya yin watsa-watsa da Atiku a 2019 – Gwamnan PDP

0

Wani jigo sannan gwamna da ake ji dashi a jam’iyyar PDP ya bayyana cewa a kullum nunawa yake cewa jam’iyyar PDP ba za ta iya kada Buhari a zaben 2019 ba saboda yadda matsaloli suka yi wa jam’iyyar Katutu.

Gwamnan wanda ya roki kada a bayyana sunan sa ya ce babu yadda za ace hakan da jam’iyyar PDP take yi game da 2019 zai cimma ruwa.

“ Yadda muke yi a yanzu haka kamar mun sadakar ne cewa baza mu ci zabe bane a 2019. A kullum shirin jam’iyyar kara tabarbarewa yake yi.

Jiga-jigan jam’iyyar na fushi cewa tun bayan nasarar da Atiku ya samu a zaben fidda gwani yayi watsi da kowa, yin abin da yaga dama yake yi ba tare da neman shawarar wani dan jam’iyya ba, ko kai waye.

Wasu daga cikin jiga-jiagan jam’iyyar dake fushi da salon jagorancin sa sun hada da gwamnonin, Gombe, Ribas, Sokoto, Sule Lamido, Ahmed Makarfi, da Rabiu Kwankwaso.

Wani babban katobara da yayi shine yin gaban kansa wajen zaban mataimakin sa batare da ya tuntubi ‘yan jam’iyyar ba.

“ ‘Yan jam’iyyar PDP basu ji dadin yadda ya yi gaban kan sa ya zabo mataimakin sa wato Peter Obi. Ko a lokacin da ya bayyana sunan Obi, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu ya nuna fushin sa karara inda yace wannan zabi bai yi ba ganin cewa shi Obi fa bai dade da sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP ba daga APGA. Ta yaya za ace wai irin shi ne za a zaba bayan ga wadanda suka bauta wa jam’iyya tun fil azal.

“ Sannan kuma bai dace ace wai daga yankin Kudu Maso Gabashin Kasar nan ne jam’iyyar zata zabi mataimakin sa ba. Ya kamata ace daga yankin Kudu maso yamma ne wato yanki Yarbawa ta zabo mataimakin nata. Domin ‘Yarbawa ba za su zabi wani ba bayan ga Tinubu da Osinbajo suna kan gaba a yakin zaben APC kuma duk daga yankin suka fito. Kyan shi da daga yankin ‘Yarbawan muka zabo mataimakin shugaban kasa da ya fi mana.

“ Sannan kuma ko shugaban Majalisar Dattawa Saraki da aka nada darektan Kamfen din Atiku din ba a yi wa ‘yan jam’iyyar adalci ba domin kuwa an manta da mutane irin su Ahmed Makarfi da irin su Sule Lamido da suka goya jam’iyyar sannan har ta tsaya da kafafunta bayan rigingimun da ta fada a baya.

Bayannan gwamnan yace, nada irin su Fayose matsayi maigirma a kamfen din matsala ce domin babu wanda zai saurari Fayose a yankin ‘yarbawa sannan Saraki ma jakar sa cike take fam da matsaloli.

Share.

game da Author