Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana wa taron ‘yan Najeriya dake kasar Poland cewa yana nan da karfin sa kuma cikin koshin lafiya.
Buhari ya kara da cewa shine dai Buharin da kowa ya sani ba wani wai Jibrin dan kasar Sudan. Ya ce wadanda suke ta yayada wannan jita-jita sun yi matukar nuna jahilcin su a fili da kuma rauni imani.
” Wani abu da ya dade ya na bani mamaki shine ganin yadda wasu suka rika yi wa mataimakin shugaban kasa fada suna neman wai ya zabe su mataimakin sa tunda ana ganin na riga na mutu a lokacin da nake kwance a gadon asibiti a Landan.
” Wannan abu yayi matukar bani mamaki. Kuma a lokacin ma sai gashi maraimaki na ya ziyarce ni a can.
Buhari ya ce ya na na daram dam cikin koshin lafiya sannan ma nan da yan kwanaki kadan zai cika shekaru 76 a duniya.
” Ni yanzu idan akwai abin da ke yawaita dauke mini hankali a gida sune jikoki na. A kullum sai kara yawa suke. Amma nine Buharin da kuka sani sannan ranar 17 ga watan nan ranar haihuwa na zai zagayo.
Buhari ya bayyana wa ‘yan Najeriya dake kasar Poland cewa gwamnatin sa ta yi matukar kokari wajen inganta fannonin ayyukan gwamnati da suka hada da kiwon lafiya, tsaro, Tattalin arzikin kasa da da raya kasa.
Idan ba a manta ba Buhari ya ta tashi zuwa kasar Poland ne domin halartar taron matsalolin sauyin yanayi da zai gudana a kasar.