Wani dan sanda ya bindige sojan sama a layin cirar kudi da katin ATM

0

Wani saje na ‘yan sanda ya dirka wa wani jami’in sojan sama bingida, ya mutu nan take a layin cirar kudi da kaftin ATM a kofar bankin Unity.

Lamarin ya faru ne a lokacin da jama’a ke kan layin cirar kudi a bakin kofar bankin, wanda ke kan titin Marian, a Kalaba, Babban Birnin Jihar Cross Rivers.

Har zuwa lokacin da ake hada wannan labari, jami’an ‘yan sanda ba su bayyana sunan jami’in su da ya yi kisan ba.

Amma dai Kakakin Rundunar ‘yan sanda ta jihar Cross River, Irene Ugbo ya tabbatar da cewa an kama wanda ya yi harbin ya na a tsare.
Sannan ya kuma shaida wa PREMIUM TIMES yadda lamarin ya faru.

“Daga abin da mu ka samu cikakken labari, wasu sojojin sama ne suka je wurin cirar kudi a layin ATM din, amma ba a cikin kakin soja su ke ba. su ma sun je ne su ciri kudi da katin ATM.

“To an ce da suka je sai suka rika rika ture jama’ar da kann layi. Shi kuma wannan dan sanda da ke aiki a bankin, sai ya ji hatsaniya ta kaure a bakin ATM, har ana turereniya.

“Da ya zo sai rudanin ya hada da shi, har wadannan sojoji da ba sanye su ke da kayan soja ba, suka yi kokarin kwace bindigar sa.

“A cikin wannan rudanin ne dan sandan ya yi harbi a sama, amma harsashe ya kuskure ya samu sojan.” Inji Ugbo.

Ya ce tuni am kama dan sandan, kuma ana bincike.

A karshe ya ce ana nan ana kokarin ganin cewa wannan sabani bai jawo rikici a tsakanin bangarorin jami’an tsaron biyu ba.

Share.

game da Author