Uba Sani ya tallafa wa matasa 512 da sana’o’i hannu a Kaduna

0

A wani gagarumin buki da aka yi a garin Kaduna na yaye daruruwan matasa da kungiyar ‘Magvoile Vocational Center tare da hadin guiwar gidauniyar Uba Sani an yi wa wadannan matasa goma na alkhairi.

A wajen bukin an yaye dalibai sama da 500 da aka koyar sana’o’i da dama da suka hada da saka, dukanci, saka jaka, ayyukan Komfuta da dai sauran su.

Dan takarar sanata na yankin Kaduna ta tsakiya, Uba Sani ya da ya halarci wannan buki ya yaba kokarin matasan da malaman su bisa kwazo da hazakar da suka nuna da kuma juriya da suka yi a tsawon lokacin da suke koyon wannna sana’a.

Duka daliban da aka yaye sun baje kayayyakin da suka yi a lokacin da suke koyon wannan sana’o’i

A jawabin na sa Uba Sani ya kara da cewa wannan kokari da aka yi soman tabi ne domin da zarar Allah ya sa yayi nasarar darewa kujerar Sanata na Kaduna ta tsakiya a majalisa dattawa zai tabbata ba daruruwa ba, dubban matasa sun more wa tallafin da zai rika badawa domin samar musu da aikin yi da abin dogaro ga.

Share.

game da Author