Tsarin Tradermoni sayen kuri’u ne -Dogara

0

Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara, ya yi tir da tsarin raba kudade da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta fantsama yi, ana kusa ga fara zabe, cewa sayen kuri’u ne ba tallafin lamune ne ga kananan ‘yan tireda ba.

Dogara ya yi wannan jawabi ne a lokacin da Kwamitin Bai-daya na Majalisar Tarayya kan INEC da Jam’iyyun Siyasa ke tattauna batun sayen kuri’u da kuma yadda za a inganta tsarin zabe a Najeriya.

Dogara ya ce ko ma wace irin kyakkyawar niyya za a yi tunanin kafa tsarin, shirin raba kudaden ya koma sayen kuri’u da kuma ribbatar jama’a a kan wanda ake so su zaba, sannan kuma rashawa ce karara.

Shi ma Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya yi irin wannan korafin da kuma zargin a kan gwamnatin tarayya, inda ya ce ta na amfani da tsarin tradermoni a fakaice ta na sayen kuri’un mutane domin zaben 2019.

Share.

game da Author