Tradermoni: Lamuni ko lamuntar kuri’u? Yadda ake samun wannan Lamuni

0

MENE NE TRADERMONI?

Tsari ne da Gwamnatin Buhari ta shigo da shi a karkashin shirin Gwmanati na Karfafa Kananan ’Yan Tireda kimanin milyan biyu a fadin kasar nan. An kuma ce lamuni ne ba kyauta ba, kuma za a bai wa kowa a bisa yarjejeniyar za ta biya, tare da gabatar da mai tsaya maka.

Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ne a sahun gaban shiga lunguna da sakon cikin kasuwannin kasar nan ya na kamfen din kaddamarwa da raba kudaden.

Yayin da wasu ke ganin alfanun abin, wasu kuma musamman ‘yan adawa na kushe tsarin cewa wani salon sayen kuri’un jama’a ne APC da gwamnatin Buhari suka shigo da shi a fakaice.

Dalilin su kuwa shi ne yadda Mataimakin Shugaban Kasa ya jajirce ya na shiga cikin kasuwanni a garuruwa daban –daban ya na kaddamar da shirin, musamman daidai lokacin da zaben 2019 ya gabato.

NAWA AKE BAYARWA?

Da farko ana raba naira 10,000. Amma idan ka kammala biyan ta, za a iya baka lamunin naira 20,000. Daga nan kuma idan ka biya, har na naira 50,000 za a iya ba ka.

Wakilin PREMIUM TIMES HAUSA ya shiga kasuwar Wuse Market a Abuja, ya binciki yadda aka yi rabon Tradermoni.

Da farko za ku bada sunayen su a karkashin kungiyoyin ku na kananan ‘yan kasuwa. Misali, kungiyar masu saida yadi ko kayan miya da sauran su.

Daga nan za ku shiga layi ana daukar sunayen su da lambobin wayar ku.
Za ka bada lambar asususun ajiyar ka na banki. Idan kuma ba ka da ita, za ka iya bada ta aboki ko dan uwa ko makwaucin ka.

Sunan ejan na TraderMoni a kasuwar Wuse II, Mista Ako. Shi ne ke tsara komai.
Daga nan mutum zai ga ‘alert’ na naira 10,000 ya shigo cikin asusun ajiyar sa ko kuma na wanda ya bayar da asusun nasa.

TA YAYA AKE BIYA?

Da yake ana raba kudin ne a karkashin Bank of Industries, to an tsara cewa duk sati wanda ya karbi lamunin zai je banki ya biya naira 420 kacal, har ya gama biyan kudin.

SU WA KE KARBA?

Wakilin mu ya fahimci cewa ko dan wace jam’iyya ana baiwa kudaden a Wuse Market, domin da idon sa ya ga wasu ‘yan jam’iyyar PDP da suka ga ‘alert’ a cikin wayar su.

“Ni dan PDP ne, kuma na nemi bashin a karkashin kungiyar mu ta masu saida yadi, na kuma samu. Domin tun sati daya kafin Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya shigo Wuse Market na ga ‘alert’”. Haka wani mai suna Hussaini ya shaida wa Premium Times Hausa a cikin Kasuwar Wuse Market.

ANA BIYA KUWA?

Sai dai kuma wani bincike da jaridar ta yi, ba ta gani ko ji wanda ya ce shi duk sati ya na zuwa banki ya na kai naira 420 din da aka ce a rika kaiwa ba.

Sannan kuma a bashin Tradermoni da aka raba a Wuse Market, da dama sun shaida wa jaridar cewa babu wanda ya tambayi adireshin su ko wani wanda zai tsaya musu.

Wasu ma cewa suka yi idan mutum bai biya ba, babu wanda zai sake tunkarar sa da maganar, amma kuma ba za a kara baka ba.

Share.

game da Author