Tsohon Shugaban Kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida ya kasance tare da matar sa, Marigayiya Maryam tsawon shekaru 40 cur. Sun yi rayuwar da sai wani yayi tunanin kamar har abada ba za su taba rabuwa ba – domin kusan ba su ma rabuwa din, saboda har lokacin da ya na shugaban kasa, duk inda ka ga Zara, to zaka ga Wata a wurin.
Sai dai kuma a ranar 27 Ga Disamba, 2009, mutuwa ta dauki ran uwargidan Babangida, Maryam, bayan ta yi fama da jiyya a wani asibiti da ke California, Amurka.
An daura musu aure a ranar 6 Ga Satumba, 1969, kuma Allah ya albarkace su da yara hudu – maza biyu, mata biyu: Mohammed, Aminu, Aisha da kuma Halima.
Tun daga ranar da ciwon kansa ya yanke rabin ran Babangida daga jikin sa, shekaru kenan da suka gabata, sai duniyar tsohon Janar din ta yi duhu.
Bai cika yawan fita ba, saboda ciwon kafa da ke damun sa. Amma kuma da ya ke Babangida kamar katangar sikari ya ke, wadda sha-zumami ke dabdala a kan ta, gidan sa ba shi rabuwa da masu ziyara.
Ko dai masu zuwa yi masa ya ka kara ji da jiki, ko kuma masu neman tubarrakin sa dangane da wani mukami da su ke nema a kasar nan. Sai kuma masu neman alfarma a inda ba su iya zuwa su nema da kan su, sais u roki Babangida ya nemar masu.
A duk tsawon shekarun da Babangida ya yi bayan mutuwar Maryam, zaman gwagwarci ya ke yi. Amma a cikin wannda tallaunawa za ku karanta, za ku ji yadda zaki ya ce ya gaji da zaman gwagwarcin da babu wata zakanya a kusa da shi, duk kuwa da cewa ya rigaya ya zama tsohon zaki, mai raruwa daga kwance…
YADDA NA YI TASHEN BALAGA TA
TAMBAYA: Ga ka dattijo dan shekaru 77 a duniya. Idan ka tuna irin yadda ka ke kyakkyawan dan saurayi a lokacin da ka ke shekaru 17 zuwa 19, shin ya ka rika fama da ‘yan mata kuwa?
AMSA: Ni dama na san sai tunanin ka ya je can. Amma bari na ba ka labarin da a cikin sa za ka iya bai wa kan sa amsa. A lokacin da na ce wa budurwar da na yi niyyar aure cewa ina son ta da aure, sai ce min ta yi: “Amma dai zolaya ta ka ke yi” Na ce ma ta ba zolaya ba ce. Sai ce min ta yi ai ita a zaton ta ni dan sheke-aya ne kawai, ba aure ne a gaba na ba. Na ce mata to ni ba dan duniya ba ne, aure na ke so na yi, domin na tattara hankali na a wuri daya, na natsu.
TAMBAYA: Ashe ka dan sheke-ayarka kafin ka natsu ka yi aure kenan?
TMABAYA: E, na dan sheke kam!
TAMBAYA: To ka dauki lokaci kafin ka shawo kan budurwar ka har ta yadda ta aure ka, domin da farko ita ta dauka kan dan sheke-aya ne kawai?
AMSA: A gaskiya bai kai shekara daya ba, ta amince, muka yi aure.
TAMBAYA: To ya ka karke da garken ‘yan matan ka a lokacin?
AMSA: Ai tilas su fahimci cewa akwai fa lokacin da tilas sai sun rabu da ni haka nan. Kuma a hakan dai suka hakura da ni din, su ka bar ni.
TAMBAYA: Kai ma ka rabu da su a lokocin kenan?
AMSA: E, na yi iyakar kokari na, na rabu da su.
TAMBAYA: Kasancewar ka musulmi, wanda addinin sa ta ba damar auren sama da mace daya. Amma sai ka tsaya kan Maryam ita kadai, tsawon shekaru arba’in, har ranar rasuwar ta, 29 Ga Disamba, 2009. Shin wace irin damuwa ka shiga kafin auren?
SHEKE-AYA MA NA DA RANAR TA
AMSA: Wato sheke-aya ma da ranar ta; saboda za ka koyi darasin rayuwa sosai.
Ya zuwa lokacin da ka nabba’a, ka natsu, ka zama kamili, to ka rigaya ka san kabli da ba’adin rayuwa, musamman a bangaren soyayya. Don haka ba mu dade mu na soyayya ba, saboda na yi dace ta na da duk abin da na ke bukata ga macen da na ke so na aura a lokacin.
TAMBAYA: Kamar me da me kenan a lokacin ka so daga macen da a ka aura?
AMSA: Ta so ni a yadda na ke. Ta amince cewa ni mutum ne, ina yin kuskure. To idan ta yi haka, ba za mu samu matsala ba kenan. sai na yi dace ta na da wadannan halaye da na ke nema.
Ina tabbatar maka a tsawon shekaru 40 da na shafe tare da Maryam, sau biyu kadai muka taba samun sabani. Ta na da jimirin jure abu, kuma iyayen ta su na da fahimtar rayuwa. A ko da yaushe ni suke goyon baya, ba ita ba.
TAMBAYA: Watakila da wani ta aura ba Babangida ba, ko kuma da ba ka kai matsayin da Allah ya daukaka ba, watakila wani abin ba za ta iya jure masa ba.
AMSA: A’a, domin ni mai yi mata kyakkyawar shaida ne. A lokacin muna fagen fama mu na Yakin Basasa, ka san akwai damuwa da rashin kwanciyar hankali ga iyalan sojoji. Za su rika rayawa a ran su shin ko miji na zai dawo? Zo ajali ne ya yi kiran sa a wurin yaki? Ko za su yi nasara? Ko abokan gaba za su kama shi?
To amma ita kwata-kwata ba ta tayar da hankalin ta. Kwai zuciyarta ta ba ta cewa sai na dawo, sai na yi nasara, ba za a kama ni ba, kuma ba zan mutu a wurin yaki ba.
ZAN SAKE AURE SABODA NA GAJI DA ZAMAN GWAGWARCI
TAMBAYA: Ya batun sake aure fa? Har yanzu ka na tunanin sake aure kuwa?
AMSA: E, ina sa ran zan sake aure. Amma dai har yanzu ina neman daidai da ni, ko kuma wadda za mu yi wa juna adalci. Saboda ba za ka yi tsammani zan auri matar da na tsere wa fintinkau a shekaru ba. Domin hakan zai haifar da matsala gare ta da kuma gare ni.
Na biyu kuma zan so na auri wadda za ta amince ta zauna da ni a yadda na ke, wanda samun hakan ya na da wahala a wannan zamanin. Shi ya sa na ce ina ta addu’a dai, kuma na san zan samu daidai da ni.
BABBAR MATSALAR DA KE DAMU NA DAGA RASHIN MARYAM
TAMBAYA: Ya ka ke fama da rayuwar gwagwarci kuwa? Mene ne babbar matsalar zaman gwagwarci?
AMSA: Na yi rashin wanda zai maida ni a kan hanya idan na kauce. Na yi rashin wanda zai ce min ‘hakan da ka yi shi ne daidai’ ko ‘hakan fa da ka yi ba daidai ba ne.’ Wannan shi ne babban abin da na rasa a rayuwar da ke ciki ta fama da gwagwarci.
JARIDAR CREST ce ta bai wa PREMUM TIMES iznin fassara wannan tattaunawa ta buga.
Discussion about this post