Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana wa taron gwamnonin Najeriya cewa kowa fa ya shiga taitayin sa domin tattalin arzikin kasar nan na cikin mawuyacin hali.
Buhari ya fadi wa gwamnonin ne a ganawar sirri da yayi da su a fadar shugaban kasa da yamman Juma’a.
Gwamnan jihar Zamfara AbdulAziz Yari wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya ya bayyana wa manema labarai bayan kammala taron.
” Buhari ya fadi mana cewa kowa fa ya shiga taitayin sa domin tattalin arzikin kasa ya fada cikin mawuyacin hali yanzu.”
Sai dai kuma Yari bai yi bayani dalla-dalla ba bisa ga abubuwan da suka tattauna da shugaba Buhari ba bayan wannan sako da ya isar wa ‘yan Najeriya daga Buhari.
” Sannan Kuma Buhari ya koka kan yadda gwamnatocin baya suka rika warwason dukiyar kasarnan kamar naman farauta.
” Buhari ya ce da a tsawon mulkin PDP shekaru 16 ba tayi tanaji ba sannan ba ta gina kasa ba. Ya ce da yanzu ba a fada cikin irin wannan matsaloli da ake fama da su ba.
Bayan haka ya shawarci gwamnonin kasar nan da su sake lale sannan su kirkiro matakai da shirye-shiryen da zai taimakawa gwamnati wajen ganin an tsamo Najeriya daga wannan matsala da ya dabaibaye kasar.