Babu shakka tarbiyan ‘ya’yan mu tana kara tabarbarewa. Hakan kuwa ya ta’allaka ne akan dalidai masu yawa. Kadan daga cikin su sune shaye-shayen kwayoyi masu gusar da hankali, misali, kodin, tramadol, wiwi da dai sauransu, kallace kallacen finafinan batsa, na cikin gida dana waje da kuma annobar amfanin da hanyoyin sadarwa na zamani musamman yanar gizo.
Har ila yau abota ta zama wata babbar annoba, sakaci na iyaye wajen tarbiyantar da yayan su.
Shaye-shayen kwayoyi masu gusar da hankali kamar su kodin, tramadol, wiwi, harda wani masifa wai matasa a yau har ruwan kwata da kashin kadangare da makamantan su suke sha don su fita daga hayyacin su.
Wannan ya sabbaba wasu halaye dake addabar al’umma kamar daba, fyade, kisan kai, sace mutane da dai sauran su. ‘Yan siyasa kuwa suan amfnai da wannan damar don cimma burin su musamman lokacin yakin neman zabe da kuma lokacin zaben.
Yawan kallace-kallacen finafinan cikin gida dana waje da basu da alaka da addini da al’adun mu yana daya daga cikin matsalolin tarbiya a wannan zamanin. Wayar hannu kuwa na daya daga cikin muhimman hanyoyin da matasa suke samun damar kallo da karba da kuma isar da sakonni masu manufofi daban-daban.
Babu shakka wayar hannun da sauran kafofin yanar gizo sun zo da alfanoni masu yawa amma a hakikanin gaskiya sun zamo kalubale ga tarbiya a yau. Hakika kuwa ya kamata iyaye mu sake karatun ta nutsu a kan kula da yadda yayan mu suke amfani da wayennan hanyoyin sadarwar da inganta tarbiyar su.
Sakaci na iyaye da rashin kula da irin abokan da yayan su suke mu’amala dasu da kuma halin da suke ciki a ko wani lokaci ma daga cikin manyan kalubalan da suke gurbata tarbiya a yau.
Ya zama wajibi iyaye su kula da irin kawaye da abokan da ‘ya’yan su suke mu’amala dasu a ko wani lokaci domin mu’amala da sa’o’I suna da tasiri akan tarbiyan yara. Yawancin lokuta, sai iyaye suna bakin kokarin su a kan tarbiya amma kawaye da abokane su ruguza wannan tarbiyar a cikin kankanin lokaci.
Saboda haka, ya kamata iyaye mu sa ido a kan irin abokai da kawayen yayan mu, muja su a jiki, muna kuma tattauna yanayin rayuwa dasu, tare da nuna musu illolin da ka iya tasowa a dalilin sakaci da addini da tarbiya ta gari. Saboda haka, ya zama wajibi iyaye mu saka ido akan irin mutanen da yayan mu suke mu’amala dasu.
Illolin tarbiya a yau baza su misaltu ba amma gaskiya abun daya kamata shine iyaye mu hankalta da cewa yanayin rayuwa ta chanza don haka kuma ya zama tilas iyaye mu ja yayan mu a jiki, mu kula da mu’amalarsu, musa ido a dukkan al’amuransu kuma mu dage da addu’a a ko wani lokaci.
Allah Ya iya mana da iyawar sa, ya kuma bamu ikon fita hakkin yayan mu na basu tarbiya ta gari don samun tsira, duniya da lahira.
Allah Ya arzurta mu da ‘yaya na gari da zasu zamo mana sadakatuj jariya ko bayan bamu.
Discussion about this post