TAMBAYA: Ina neman Bayani game da Saka Al-Kur’ani a waya, Tare da Imam Bello Mai-Iyali

0

TAMBAYA: Yaya hukuncin saka Qur’ani a waya a musulunci? Akan kalli batsa a
wayar, akan turo batsa baka sani ba ma, sannan kuma akan shiga bayi dashi. Ina neman Bayani game da Saka kur’ani a waya.

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi
Muhammad SAW. Hakika wannan zamani ne na kimiyya da fasaha (technology), kimiyya ta mamaye komai, da alhairinta ko sharrita.

Daga cikin alhairinta akwai sanya Al-Kur’ani a cikin na’ura kamar wayar hannu. Yawaitar kimiyya yasa mutane na ta tambayoyi domin sanin Halal
da Haram a cikin addinin mu. Ina rukun Allah da yakarama mai tambaya Ilimi, fahimta da dacewa akan kyakkyawan aiki.

Babu laifi a sanya Al-Kur’ani a na’ura mai kwakwalwa ( kamar away a cassetes, CD/DVD plates, flash, computers etc).

Amma wajibi ne a tsare alfarmansa da darajarsa akan hakan.

Hukuncin mu’amala da batsa nanan akan Haramci, saidai baishafi Al-Kur’anin da ke cikin waya ba. Duk da cewa suna cikin waya daya, to amma ko wanne yana mazauninsa.

Sai dai idan hakan yana taba darajar Al-Kur’anin da ke cikin wayar, to ayi gaggawan tsare martabar Al-Kur’ani, tahanyar kawar da batsar a cikin wayar. Antsinewa duk mai kallon tsiracin wani.

Mas’alar shiga bayi da na’ura ko wayar da ke dauke da Al-Kur’ani ta kasu gida biyu:

1 – Makaruhi ne a shiga da wayar ko na’urar da ke dauke da Al-Kur’ani
idan gilashin na’urar/wayar na bude da Al-Kur’anin kuma ana ganinsa a
gilashin (screen).

Malamai sunce yin hakan kamar shiga da Al-Kur’ani ne bayi. Kuma haka ya sabawa shari’ah, hasilima wasu malam sun haramta kai tsaye, domin rashin dacewarsa.

2 – Kauli na biyu shin ne halacci (Halal) idan gilashin wayar baya nuna
(displaying the text of Qur’an) ayoyin Al-Kur’ani a fili. Ko kuma wayar na kashe (swich off), ko tayi lumm da duhu ba’a ganin komai na Al-Kur’ani a gilashinta. To, idan gilashin wayar bai nuna Al-Kur’ani ba, babu komai.

Sharadi ne sai mai tsarki zai dauki Al-Kur’ani, to shin tsarki sharadi ne game da Al-Kur’anin na’ura (kamar waya)?
Mafi yawan malamai na ganin cewa bai dace musulmi yabude Al-Kur’anin wayarsa ba sai yanada tsarki (ma’ana babu haila ko janaba), domin hakan kamar daukar Al-Kur’ani ne cikkake. Amma wasu malamai suna ganin babu komai matukar mutum ba zai taba gilashin (screen) da ke nuna rubutun ba.

Mas’alar sanya Al-Kur’ani a matsayin sautin kirar waya ko sautin fadakarwa… (ringing /caller tone, alert, alam etc..). Malamai sun tafi akan haramcin sayan Kira’a (karatun Al-Kur’ani) a matsayin sautin waya.

Mas’alar karatun Sallah ta hanyar na’ura (kamar waya) wato kamar sallar Asham ko Tahajjud ta hanyar bude Al-Kur’anin da ke cikin waya ana karantawa. Malamai sunyi sabani akan haka:

1 – An hana karatun Sallah ta hanyar na’ura kuma hakan ya bata Sallah.

2 – An hana karatun Sallar Farilla kawai ta hanyar na’ura.

3 – Halal ne Karatun Sallah ta hanyar na’ura ( Sallar Farillace ko ta Nafila duk sun halatta).

4 – Makaruhi ne (abin kyama abin ki) yin karatun sallah da Al-Kur’anin waya, amma Sallar tayi.

Abinda yafi shi ne mutum yayi karatu daga abinda ya hardace, amma idan ya bude Al-Kur’anin wayarsa sannan yayi karatu daga cikinsa babu komai.

Allah shi ne mafi sani.

Share.

game da Author