TAMBAYA: Hukuncin mace da ta yi sallah da matsattsen kaya da kuma gashin ta a waje, Tare da Imam Bello Mai-Iyali

0

TAMBAYA: Hukuncin mace da ta yi sallah da matsattsen kaya da kuma gashin ta a waje, Tare da Imam Bello Mai-Iyali

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Allah ya umurci bayin sa da yin ado yayin Sallah (Suratul A’arafi aya ta 31), malamai suka ce mafi karancin ado shi ne suturta al’aura.

Saboda haka ne ma suturta al’aura ya zamo sharadi a Sallah. Sallah ba ta ingantaba face masallacin ya suturta al’aurarsa. Ba ason musulmi yayi Sallah da kayan barci, ko kayan aiki, ko kaya masu datti, Allah kyakkyawa ne kuma yana son ado.

1 – Macce dukkan jikinta al’aura ne har gashinta. Wajibi ne kenan ta rufe shi a cikin Sallah da wajenta. Idan macce tana Sallah sai
gashinta ya bayyana (ya bude) kuma tayi gaggawan rufe shi nan take, to babu laifi a cikin hakan, sallar ta tayi. Amma idan tayi Sallah da gashinta abude don jahilci, to babu sallar kuma za ta rama wannan sallar. Hakanan kuma idan tayi Sallah da gashinta a bayyane don rashin sani (ma’ana bata san gashinta yana bude ba) ko mantuwa, babu Sallah kuma za ta rama sallar.

2 – Sharadi ne macce tarufe dukkan jikinta yayin Sallah, tun daga kanta har kafan ta. Idan mace ta lullube jikinta da sura wanda baya bayyana wata gaba nata, to sallarta tayi. Saidai abinda akafi so shi ne a sanya sutura mai kauri, mai yalwan da baya bayyana surar jikin macce.

3 – Idan macce ta sanya matsatsun tufafi mai nuna suran jikinta ta yi Sallah da su, sallar ta tayi amma fa ta saba umurnin shari’ah na
sanyan suturar kamala yayin Sallah, laifinta na sanya matsatsun kaya kuma na nan a kan ta.

Makaruhi ne yin Sallah da matsatsun kaya ga
na-miji da macce. Kuma hakan na iya kai ga Haramci. Sai dai Sallah tayi.

Allah Shi ne mafi sani.

Share.

game da Author