TAMBAYA: A wane zamani ne musulunci ya hana kwarkwara da ajiye su a gida. Shin yana da kyau ko a a?
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.
Mas’alar bauta, bayi da kwarkwara mas’ala ce da makiya musulunci suke aibata musulmi da ita. Lalle harkar bayi tsohuwar harkace da musulunci ya gada kuma bauta ta wanzu a cikin al’ummomin duniya rankatakaf, ashe kenan ba gajiyawar musulunci ba ne.
Da musulunci ya zo, sai ya shinfida kyawawan tsari a cikin harkan bayi da bauta, kuma ya takaita hanyoyin samun bayi zuwa kwaya daya tak, wato hanyar JIHADI, sannan kuma ya yawaita hanyoyin ‘yanci. Musulunci ya kwadaitar da ‘yanta bayi kuma ya sashi a matsayin daya daga cikin manyan ibadu, ‘yanta bawa kaffarar kisa ne, kaffarar karya azumin Ramadana ne, kaffarar Zihari ne, kaffarar rantsuwa ne, kuma musulunci ya samo ma bayi ‘yancin mutuntaka.
Kuma musulunci ya hukunta cewa duk wata kwarkwarar da ta haihu da ubangidanta, toh ‘yantacciyace, kuma ‘ya’yanta ma ‘yantattu ne.
Babu wani lokaci da musulunci ya haramta bauta, bayi, kwarkwara ko sa daka. Halal ne a musulunce da nassoshin Al-Kur’ani da Sunnan ma’aiki SAW. Wata kila sabo da rubdugun da makiya musulunci ke yi wa musulmai da musulunci, mai tambaya ke zaton musulunci ya haramta wannan mas’ala ta bauta, bayi da kwarkwara, ko kuma yake tunanin ai ya kamata musulunci ya haramta.
Hakika musulunci ya dakushe harkar bauta da bayi harma da kwarkwara, amma babu inda musulunci ya hana, mas’alar na nan matsayin halal, matukar ana Jihadi na gaskiya. Idan anci nasara akan ARNA/MAGUZAWA a jihadi, toh, shugaba na iya zantar da bautar da su, ko su fanshi kansu, ko duk wani hukuncin da yadace da su.
Ana iya mallakar bawa/baiwa ta hanyan jihadi (idan shugaba ya raba ganimarsu ga mujahidai) ko a saya daga wanda ya mallaka. Kuma duk wanda ya mallaka ta kowace hanya daga cikin hanyoyi biyu (hanyan jihadi ko saya da kudi) ya hallata yayi kwarkwara da su.
A kashin gaskiya a zamanin mu na yau, lamari ne mai kamar wuya a mallaki bayi/kwarkwara ta hanyan da shari’ah ta shimfida. Domin Musulmai sun watsar da harkan Jihadi, ga rashin shugabanci na musulunci, ga raunin imani, ga kwadayin duniya, ga dunkulewar doniya guri guda da sauran matsalolin zamani.
Bugu da kari kuma, kasashen musulmi sun rattaba hannu akan kundin haramta bauta na duniya wanda aka amince da shi a shekarar 1953.
Shugabanin musulmi sun amince da haramcin bauta, bayi da kwarkwara da yarjejeniyar majalisar dinkin duniya. Hakan kuma na alamta cewa bauta, bayi da kwarkwara sun haramta gare mu.
Sabo da haka lalle ne musulmi suyi taka tsantsan a cikin mas’alar bauta, bayi da kwarkwara.
Allah shi ne mafi sani.