TALLAFIN MAI: Yadda Kamfanin NNPC ya yi asarar naira bilyan 623.17 da sunan tallafi a cikin 2018

0

Gwamnatin Tarayya ta biya har naira bilyan 623.17 da sunan tallafin mai cikin 2018, tsakanin Janairu zuwa Nuwamba, kamar yadda wani bayanin jimilla da dalla-dallar kudaden da kamfanin man fetur na NNPC, mallakar gwamnati ya nuna.

Takardun wadanda suka fado hannun PREMIUM TIMES, su na daga cikin bayanan da NNPC ta gabatar wa Kwamitin Kasafta wa Gwamnatin Tarayya, ta jihohi da kwananan hukumomi kudade cikin makon da ya gabata.

NNPC ta yi bayanin cewa an kashe kudaden da sunan tallafi. Ta yi bayanin ne a lokacin zaman da kwamitin ya yi domin kasafta kudaden watan Nuwamba na 2018 da ya gabata.

An kashe kudaden ne kamar yadda bayanin ya wallafa a ranar 19 Ga Disamba, 2018, cewa;

Daga cikin naira bilyan 676.49 da bayanan suka nuna, an ce an kashe naira bilyan 599.7 wajen biyan tsarin nan da NNPC ke kira DSDP, sauran naira bilyan 23.4 kuma an kashe su ne matatun mai hudu na Najeriya da ke Warri, Fatakwal da kuma Kaduna.

Wannan tsari da NNPC ta rada wa suna, ya na nufin madarar kudaden da NNPC ta kashe a madadin Gwamnatin Tarayya wajen shigowa da kuma raba man fetur wanda ake sha a nan cikin gida.

A takaice kudade ne da ake kashewa fiye da ladar saukale da lodin mai, wadanda idan aka tattara abin da ake kashe wa lita daya tun daga dakon ta daga kasashen Turai har saukalen ta a tashar jiragen ruwan mu da kuma lodin ta zuwa rumbunan adana fetur da rabawa ga dillalan mai har zuwa lokacin da direba zai sha a gidan mai ya mika kudi, to wahalar da ake yi wa lita daya ta fi karfin a sayar da ita naira 145.

Shi kuma tsarin DSDP, ya na nufin kudaden da gwamnati ke biya a matsayin tallafi daga tsarin sayar da ruwan danyen mai zalla ga dillalai ko ‘yan kasuwar mai na nan gida domin tacewa su sayar.

A wannan tsari ne gwamnati ta ce ta sayar musu da gangar danyen mai 445,000.

Ita kuma wannan sabat-ta-juyat-ta, NNPC na saida musu danyen mai ne nan a gida, su kuma su yi lodi su fitar waje su tace, su maido nan cikin gida Najeriya su sayar.

A cikin 2016 ne gwamnatin Muhammadu Buhari ta shigo da wannan tsari, sabanin tsarin musanye da gwamnatin Jonathan ta shigo da shi saboda rashin iya tace danyen mai da matatun mai na Najeriya suka kasa yi.

HADA-HADAR DA BABU RIBA SAI FADUWA

NNPC dai shi kadai ne ke shigo da tataccen man fetur daga kasashen ketare zuwa cikin gida Najeriya domin amfanin masu ababen hawa.

Tun kafin Shugaba Buhari yah au, y ace idan ya yi nasara zai gaggauta gyara matatun mai na Najeriya domin a daina dibga asarar fita da mai ana tacewa a waje, sannan kuma sake shigo mana da shi nan gida.

Sai dai kuma kusan shekaru uku da rabi bayan hawan sa, har yau ba ta canja zani ba.

Kukumar ta bada rahoton karin kudin da ke shafar NNPC wajen aikin shigo da mai kama tun daga karin kudin saukale daga jiragen ruwa da kuma kudin sake loda shi a raba a cikin kasa.

FARASHIN FETUR: AN KI CIN BIRI AN CI KARE

Bugu da kari kuma farashin lita daya a kan naira 145 da gwamnati ta tsaida, shi ne ya yi wa tsarin kiki-kaka, domin a halin yanzu kamata ya yi a ce ana saida lita daya a kan naira 185, wanda wannan farashi ne idan aka sayar a haka, to gwamnati ba za ta yi asarar ko naira biyar a kowace lita ba kenan.

Idan ba a manta ba, a cikin watan Maris da ya gabata, NNPC ta bayyana cewa a kowace rana ta na yin asarar naira milyan 774 ta hanyar cika kudaden da ke yin gibi idan an saida litar man fatur a kan naira 145.

Har ila yau, NNPC ya ce shi ke biyan kudaden da gumin jikin sa, ba tare da samun taimako ko na sisi ba daga gwamnatin tarayya.

Idan ba a manta ba kuma, ranar 16 Ga Oktoba, Majalisar Dattawa NNPC ta biya kudaden tallafi har dala bilyan 3.5 da amincewar Shugaba Muhammadu Buhari, ba tare da sanin Majalisa ko amincewar ta ba.

Sannan kuma a ranar 5 Ga Nuwamba, PREMIUM TIMES ta bada rahoton musamman kan yadda NNPC ta rika yin abin nan da ake kira a kwashi kudin Lado a biya bashin da ciwo a hannun Ladan.

NNPC ta rika kwasar har dala bilyan 1.05 daga Asusun Tara Ribar Gas na Gwamnatin Tarayya, wato NLNG, ta rika biyan kudaden tallafi da su.

Da farko da an karyata labarin, amma da PREMIUM TIMES ta tsaya kan bakan ta, daga baya sai Shugaban NNPC mikanti Baru ya fito ya ce gaskiya ne, an debi kudaden daga Asusun NLNG an biya tallafin fetur da su, amma da masaniya da kuma amincewar shugaban kasa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya hau mulki ne ya samu ana saida litar man fetur naira 87, kuma ya yi alkawarin samun saukin tsadar da fetur ya yi ga talakawa.

Sai dai kuma shekarar daya tal bayan hawan sa, fetur ya yi tashin-gwauron-zabo, ya koma naira 145. Sannan kuma aka rika biyan tallafin da shi Buhari ya ce ya soke, sanadiyyar karin da aka yi wa farashin kowace lita daya ta fetur.

Share.

game da Author