SUNAYE: Rundunar ‘Yan sanda ta kori jami’an ta 121 da suka ki zuwa filin daga da Boko Haram

0

Kwanaki kadan bayan bankado wani rufa-rufa da rundunar ‘yan sandan Najeriya ke yi na wasu jami’an su 167 da suka gudu da makaman su a hannu bayan an tura su filin daga da Boko Haram, PREMIUM TIMES ta sake gano cewa a makon da ya gabata rundunar ta sallami wasu har 121 cikin su daga aiki.

Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES ta wallafa sunayen wasu ‘yan sanda da suka waske da makaman su bayan an tura su filin daga da Boko Haram.

Wadannan ‘yan sanda wadanda aka yi kururuwar neman su ruwa a jallo, za su fuskanci hukunci mai tsanani idan aka kama su.

Su na cikin jami’an ‘yan sanda 2,000 wadanda Sufeto Janar ya tsamo, domin kai daukin taimaka wa sojoji wajen yaki da ta’addanci.

An kuma tabbatar da cewa a lokacin da suka arce, babu daya daga cikin su wanda ya damka bindigar da ke hannun sa ko harsasai.

Wanda hakan kamar yadda PREMIUM TIMES ta kalato, wata babbar bazarana cewa matuka.

An dai tura su ne a Makarantar Horas da ‘Yan Sanda ta Musamman da kwe Buni Yadi, Jihar Yobe.

Sai dai kuma a lokacin da suka samu labarin cewa za a tura su ne domin su yi yaki da Boko Haram, musamman a kan iyakar Najeriya da Nijar da kuma Kamaru, sai suka fara sulalewa su na gudu tun cikin makon da ya gabata.

Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan sandan na Mobile na tunanin fadawa cikin irin halin da wasu sojoji suka rika shiga inda wasu manyan jami’an su ke yin kashin-dankalin da aka karshe su kananan jami’an da ak e turawa ne sa kan rasa raukan su a hannun Boko Haram.

A cikin haka ne kuma rundunar ta saka ta kori 121 cikin su duk a boye.

Ga sunayen wadanda aka kora;

Share.

game da Author