SSS ta mika mai tsaron Aisha Buhari da ake zargin yin sama da fadi da biliyoyin naira ga ‘Yan sanda

0

Hukumar tsaro na SSS ta mika mai tsaron Aisha Buhari, Sani Baba Inna da take tsare da ga hukumar ‘yan sanda domin ci gaba da binciken sa zargin sama da fadi da biliyoyin naira da ya yi na kyauta da ake ba uwargidan Shugaban Kasa.

Shi dai Baba Inna ana tsare da shine a bisa zargin karbar kudade daga hannun ‘yan siyasa da wasu manyan ‘yan kasuwa da sukan yi wa uwargidan shugaban Kasa Aisha kyauta, kudade da suka kai sama da naira biliyan 2.

Ko da aka fara gudanar da wannan bincike an gano cewa babu irin wadannan kudade a asusun ajiyar Baba Inna amma duk da haka SSS suka tasa keyar sa inda sai yanzu suka sake shi.

A wancan lokaci an gano cewa rundunar ‘yan sanda sun gudanar da bincike akai kuma ba a same shi da laifi ba.

Ko da yake ita kanta uwargidan Buhari a wasika da ta rubuta ta bayyana cewa daga ofishin ta wanda mai taimaka mata kan harkokin yada labarai Suleiman Haruna ya saka wa hannu ta ce
Sani wanda ya fara aiki da ita tun a 2016 ya rika a amfani da sunan ta wajen karbar kyaututtuka wajen mutane.

Ta ce tana da masaniya game da munanan aiyukkan Sani amma kama shi da jami’an tsaro suka yi ne ba ta sani ba.

Daga nan Aisha ta kuma tabbatar da cewa ita ko ‘ya’yan ta basu taba aika wani ma’aikaci ya karbo musu alfarma ta kowacce iri daga hannun wani ba.

Yanzu dai ‘yan sanda zasu ci gaba da bincikken Sani Dan Inna

SHARE.

Share.

game da Author