Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Musawa da Matazu na Jihar Katsina, Hon. Ibrahim Murtala, ya fice daga APC ya koma PDP.
Murtala ya yi wannan bayanin ficewa ne a cikin wata wasika da Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara ya karanta a zauren Majalisa.
Murtala dai bai bayyana dalilin ficewar sa daga APC ba.
Shi ne na farko daga jihar da Shugaba Muhammadu Buhari, ya fito da ya fara tsallake shingen APC ya dira PDP ko wata jam’iyya.
Zaben fidda-gwanin APC ya haifar da rikice-rikice a cikin jam’iyyar wanda hakan ya yi sanadiyyar ficewar wasu da dama, wasu kuma suka maka shugabannin jam’iyyar kotu, ana ta tafka shari’u barkatai.