Sama da matasa 100,000 ke neman aikin daukar ’yan sanda 10,000

0

Hukumar Kula da Aikin ‘Yan sanda ta Kasa, PSC ta ce ta karbi takardun neman aiki na matasa 104,289, bayan buga sanarwar neman daukar aikin ‘yan sanda dubu 10,000 kacal da ta yi.

Hukumar ta cika da mamakin yadda a cikin kwanaki biyar kacal bayan yin sanarwa da kuma bude shafin intanet da ake shiga a cika fam, ta samu sunayen matasa har 21,878.

Shugaba Muhammadu Buharfi ne ya amince da daukar ‘yan sanda 10,000 domin karfafa tsaro a fadin kasar nan.
Kakakin Yada Labarai na Hukumar PSC, Ikechukwu Ani, ya ce an samu sunayaen 104,289 ac cikin kwanaki 12 bayan yin sanarwar a ranar 30 Ga Nuwamba.

Ya zuwa ranar Talata 1:30 daidai ne aka samu yawan sunayen matasa 104,289 din.

Ya ce za a rufe karbar sunaye da fam na masu neman shiga aikin dan sanda din a ranar 11 Ga Janairu, 2019.
Daga nan sai y ace jihar Neja ce ta fi sauran jihohi yawan masu, sai Kano sai Katsina sai kuma Bauchi.

Share.

game da Author