Shugaban hukumar hana yaduwar cutar Kanjamau (NACA) Sani Aliyu ya bayyana cewa hukumar za ta gabatar da sakamakon kirgen yawan mutanen dake dauke da cutar kanjamau a Najeriya a watan Maris din 2019.
Aliyu yace sakamakon zai taimaka wa gwamnati wajen daukan tsauraran matakai wajen hana yaduwar cutar da inganta kulan da wadanda ke dauke da cutar suke samu.
Ya ce a yanzu haka sun kammala gudanar da binciken a jihohi 27 a kasar sannan idan har dai aiki ya ci gaba da tafiya kamar haka za su kammala binciken a watan Disamba.
A karshe jami’in hukumar hana yaduwar cutar kanjamau da cututtukan sanyi na gwamnatin tarayya Araoye Segilola yace har yanuza dai akwai mutane da dama da basu da masaniya game da matsayin su.
Discussion about this post