Wani likitan mata mai suna Imran Morhason-Bello ya bayyana cewa saka yatsa ko kuma yatsu da yin amfani da sabulu wajen wanke al’aura na rage wa mace jin dadin jima’i.
Ya ce yin hakan na sa a kamu da cututtukan da idan ba an gaggauta yin maganin ba ka iya hana mace jin dadin jima’i.
Morhason-Bello ya fadi hake ne a taron wayar da kan mutane game da illolin yi wa mata kaciya da aka yi a Abuja ranar Laraba.
Likitan ya ce kamata ya yi a wayar da kan mata game da yadda za su rika tsaftace al’aurar su ba tare da sun cutar da kan su ba.
” Mata da dama kan fada cikin irin wannan matsala ne a dalilin wai don su tsaftace gaban su.
Morhason-Bello yace mace za ta iya tsaftace al’auran ta da ruwa mai tsafta kawai ba tare da ta yi amfani da sabulu ba ko kuma ta saka yatsun ta a gaban ta ba.
A karshe ya kuma kara yin kira ga mata da su rika yin hankali wajen aske gashin gaban su domin wajen yin haka na iya sa a ji rauni wanda ka iya hana mace jin dadin saduwa da namiji.
” Kare al’aura daga samun rauni na daga cikin hanyoyin guje wa matsalolin rashin jin dadin jima’I da kauce wa kamuwa da cututtuka da dama.