SABON SALO: Hafiz Abubakar, Aminu Dabo, Danjuma Dambazau sun dawo APC

0

Idan ba a manta ba tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano Hafiz Abubakar ya yi murabus daga kujerar mataimakin gwamna Abdullahi Ganduje inda daga bisani ya canja sheka daga APC zuwa jam’iyyar PRP domin yin takarar gwamnan jihar Kano.

Hafiz Abubakar dai rikakken aminin tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ne a siyasan ce wanda koya yayi zaton ficewar sa daga APC zai sa ya samu kujerar takarar gwamna a jam’iyyar PDP.

Da hakan bai yiwuba sai ya buge da yankar tikitin zama dan jam’iyyar PRP.

Bayan haka ne fa wasu da dama daga cikin jiga-jigan ‘yan jam’iyyar APC suka fice daga jam’iyyar domin nuna rashin jin dadin su da yadda gwamna Ganduje yake gudanar da shgabancin jam’iyyar a jihar.

Sai dai kuma a wani sabon salo da ya auku ranar Laraba, inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika da jirgi na musamman domin ya taho da Hafiz Abubakar, Aminu Dabo, Danjuma Dambazau, Mu’azu Magaji da Sanata Isa Zarewa zuwa fadar shugaban kasa domin ganawa ta musamman.

A ganawar, Buhari ya roki hasalallun ‘yan siyasan da su yi hakuri su dawo jam’iyyar APC domin a hada karfi wuri daya a kada PDP a jihar Kano da kasa baki daya.

Buhari ya ce lallai gwamnatin sa za ta duba inda aka tafka kura-kurai musamman ga ‘yan siyasa domin kada hakan ya sake faruwa.

Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru ne ya jagoranci wadannan ‘yan siyasa zuwa fadar shugaban kasa domin ganawa da shugaba Buhari.

A can jihar Kano kuma, Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi alkawarin yin aiki da duka wadanda suka dawo domin ci gaban jam’iyyar.

Jihar Kano dai ita ce ta yi wa buhari ambaliyar kuri’u a 2015 da babu wata jiha da ya samu irin haka.

Wannan sauyi da ka samu zai yi matukar tada wa Sanata Rabiu Kwankwaso hankali ganin cewa dukkan su dai mutanen sa kuma na gaban goshin sa da yake tunkaho da su a siyasan ce.

Share.

game da Author