RIKICIN JIGAWA: Bello Maitama ya sha da kyar a hannun matasan Gwaram

0

Tsohon ministan ciniki, Bello Maitama ya sha da kyar a hannun matasan karamar hukumar Gwaram inda suka far wa gidan sa sannan suka tarwatsa taron sulhunta wasu ‘yan siyasa da ya ke jagoranta.

Gwamnan jihar Jigawa Mohammed Badaru ya nada sanata Bello Maitama ya jagoranci kwamitin sulhunta ya’yan jam’iyyar APC da basu ga maciji a karamar hukumar Gwaram.

Tun bayan nada sabon shugaban karamar hukumar Gwaram Abdulmalik Shehu, aka yi ta samun rashin jituwa tsakanin magoya bayan shugaban Karamar hukumar da wasu ‘yan siyasa.

Wani da abin ya faru a idanuwar sa ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa matasa sun far wa gidan sanata Maitama inda ake taron sulhu na ‘ya’yan jam’iyyar APC.

Tare da shi sanatan akwai Kakakin majalisar jihar Isa Idris da shima da kyar ya sha.

Bayanai sun nuna cewa da kyar aka samu aka gudu da Maitama da Isa.

Share.

game da Author