A wani sabon yunkuri da Shugaban APC na Kasa, Adams Oshiomhole ke ganin zai iya karya lagon gwamnonin Imo Rochas Okorocha da na Ogun Ibikunle Amosun, shugaban na APC ya rusa Kwamitin Zartaswa na jam’iyyar APC a jihohin biyu.
Okorocha a Amosun dai sun raba hanya da jam’iyyar APC a tsarin shugabannnin ta. Har suka sha alwashin ba za su mara wa ‘yan takarar gwamnan APC na jihohin su domin su yi nasara a zaben 2019 ba.
Wadanda aka rusa din sun kuma shafi har da shugabannin zartaswa na kananan hukumomin jihohin na Ogun da Imo.
Sakataren Yada Labarai a APC na Kasa, Lanre Issa-Onilu ne ya shaida wa PREMIUM TIMES Haka a yau Laraba.
Ana zargin shugabannin da aka rusa din duk su na goyon bayan gwamnonin ne, wadanda su kuma gwamnonin ba su goyon bayan jam’iyyar su ta APC ta yi nasara a zaben gwamna a jihohin na su, wato Imo da Ogun.