RIKICIN APC: Dattin jiki ma karin karfi ne, wanda bai sani ba ke wanka -Oshiomhole

0

Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole, ya ce rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar tun bayan zabukan fidda-gwani, alama ce da ke nuna cewa APC dimokradiyya na aiki sosai, yadda mambobin jam’iyyar na da damar bayyana ra’ayoyin su da abin da ke damun su.

Oshiomhole ya yi wannan bayani jiya Litinin a lokacin da ya ke karbar Kwaminin Sasanta Rigingimun APC na Arewa maso Gabas, a karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Nassarawa, Tanko Almakura.

Oshiomhole ya yaba wa mambobin kwamitin saboda gaggawar daukar matakan da duk suka kamata domin su ne kwamitin farko daga cikin kwamitoci shida da aka nada domin magance matsalolin da suka danne jam’iyyar APC.

Oshiomhole ya ce matsalolin da APC ta shiga, ba su nuna cewa jam’iyyar ta fita daga hayyacin ta ba, amma sun nuna cewa abubuwa ne da dukkan jama’a da ita kanta jam’iyyar za su yi koyi daga abubuwan da suka faru din.

“Dama mun san za a iya samun wadannan da ma kowadanne irin rikice-rikice na cikinn gidan jam’iyyar. Amma fa ba su na nufin jam’iyyar ta fita daga hayyacin ta ba ne. Za mu ma iya koyo daga korafe-korafen masu kuka daga masu nuna rashin jin dadin abin da ya faru da su, a gaba kuma sai mu gyara.”

Daga nan ya ce APC ta shuka abin koyi ga zaben fidda-gwani, domin ba ta bayar da tikitin zabe kai-tsaye ba, sai da aka yi gwagwagwa tukunna. Har ya bada misali da rashin zaben da aka yi wa gwamnan jihar Lagos, Akinwumi Ambode a karo na biyu.

Share.

game da Author