Rashin sinadarin Vitamin D na kawo cutar ‘Schizophrenia’ – Bincike

0

Wasu likitoci daga jami’ar Queensland dake Brisbane kasar Australia sun gano cewa rashin sinadarin ‘Vitamin D’ a jiki na kawo cutar ‘Schizophrenia’.

Schizophrenia cuta ce wanda idan aka kamu da ita mutum kan zama musaki.

Bayanai sun nuna cewa an fi kamuwa da wannan cuta a kasashen ko kuma wuraren da ake rashin samun hasken rana.

Alamun kamuwa da wannan cuta sun hada da rashin iya motsa jiki,rashin iya magana,rashin iya gane magana da sauran su.

Likitocin sun bayyana cewa binciken da suka gudanar ya nuna cewa jariran da aka haifa da matsalar rashin isasshiyar sinadarin Vitamin D na iya kamuwa da wannan cutar idan sun girma.

Domin guje wa kamuwa da cutar likitocin suka yi kira ga mutane kan cin abincin dake dauke dauke da sinadarin Vitamin D.

Share.

game da Author