Rashin saka hannu a dokar Zabe da Buhari ya yi daidai ne – Sanata Ahmed Lawan

0

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya bayyana cewa shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi daidai da kin saka hannu a dokar zabe da majalisar kasa ta mika masa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya maida wa majalisar kasa dokar yana mai cewa akwai wurare da dama da bai amince da su ba da wanda majalisar kasa ce ta sauya su.

Ahmed Lawan da ya goyi bayan shugaban kasan ya bayyana cewa Buhari bai yi laifi ba don yaki saka hannu a wannan doka.

” Idan har shugaba Buhari ya ga bai gamsu da gyarar da majalisa tayi wa dokar ba yana da ikon kin saka hannu. Hakan ba zai taba zama matsala ba ko kuma ya kawo wa kasa cikas ga zaben da ke tafe.

” Dokar da aka yi amfani da shi a 2015 na nan daram. Babu abin da ya same shi. Za a iya amfani da shi a gudanar da zaben 2019. Hakan bai saba wa dokar kasa ba. Hasali ma an yaba wa kasar nan bisa ga yadda aka gudanar da zaben 2015.

” Za mu iya yin amfani da wannan doka in ya so daga baya a sake duba wannan doka.

An dade ana ta kai ruwa rana tsakanin majalisar Kasa da fadar shugaban kasa bisa ga wannan gyara da aka yi wa dokar zaben. Jam’iyyar adawa, PDP, ta zargi gwamnatin Buhari da toshe kunnuwar sa a duk lokacin da aka tado maganar gyaran dokar zaben.

PDP ta ce Buhari na yin haka ne domin samun damar yin murdiya a zaben 2019.

Share.

game da Author