Hukumar Kididddiga ta Kasa, NBS, wadda ta Gwamnatin Tarayya ce, ta bayyana cewa rashin aiki ya karu matuka a kasar nan.
NBS ta ce a karshen 2017, kashi 18 bisa 100 na majiya karfi na su da aikin yi. Yanzu kuwa a karshen 2018, kashi 23 bisa 100 ne ba su da aiki.
NBS ta kara da cewa yawan ‘yan Najeriya majiya karfin iya yin aiki ya karu daha milyan 111.1 zuwa milyan 115.3. Wadannan adadi inji hukumar, duk ‘yan daga shekaru 15 ne zuwa 64.
Hukumar ta kuma yi tsokacin cewa a karshen 2015 akwai masu bukatar yin aiki har milyan 75.94.
A yanzu karshen 2018 kuwa, ta ce yawan su ya kai milyan 90.5.