Ragwargwabewar gwamnati rashin aiki da ta’ammuli da kwayoyi suka assasa ta’addanci a Zamfara – Minista Dan-Ali

0

Ministan tsaro Mansur Dan-Ali wanda dan asalin jihar Zamfara ne kuma dan asalin karamar hukumar Birnin Magaji da hare-haren ‘yan ta’adda yayi wa katutu ya bayyana cewa ragwargwabewar gwamnati a jihar Zamfara, yin ta’ammuli da kwayoyi da rashin aikin yi da natasan jihar ke fama da ne ya assasa rashin zaman lafiya da ayyukan ta’addanci a jihar.

Idan ba a manta ba jihar Zamfara ta dadr tana fama da rashin zaman lafiya a dalilin ayyukan mahara da masu yin garkuwa da mutane.

Zuwa yanzu an kiyasta cewa akalla mutane sama da 3000 sun rasa rayukan su a sanadiyyar hare-haren mahara da taki ci yaki cinyewa.

Wani mazaunin daya daga cikin kauyukan Zamfara ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa mutanen jihar suna ciki matsanancin Kangi matuka.

Mazaunin yace maharan sun far wa kauyen Garin Haladu inda suka kashe manoma 12 a gonakin su da karfe daya na ranar Laraba.

” Da yamma kuma sai suka sake shiga wasu kauyukan dake kusa da wadannan kauyen inda suka kashe wasu mutanen kuma.

” A lissafe maharan sun kashe mutane 12 a Garin Haladu, hudu a Nasarawa Godal sannan a Garin Kaka suka kashe mutane tara.

Mazaunin yace a dalilin wannan hari da dama sun sami rauni a jikinsu sannan suna samun kulan da suke bukata a asibiti.

Bayanai sun nuna cewa wannan ba shine karo na farko ba da mahara ke kai wa kauyukan jihar Zamfara hari.

Hare-hare irin wannan ya hana mazaunan kauyukan Ballaka, Tsalle, Gidan Kare, Katsinawa, Garin Boka da Garin kaka sakat inda gaba daya sun koma hedikwatan karamar hukumar Birnin Magaji.

A yanzu dai kananan hukumomin da suke yawan fama da wannan matsalar sun hada da Tsafe, Zurmi, Shinkafi, Maradun, Maru da Birnin Magaji.

Mansur Dan-Ali ya ce gwamnati ta aika da jami’an tsaro na soji da ‘yan sanda suwa sassa da dama a jihar.

Ya ce ba sojojin kasa ba, ma’aikatan tsaro ta aika da dakarun sojin sama domin ganin an dakile ire-iren wadannan hare-hare.

Sai dai kuma duk da irin wannan kokari na gwamnati abin dai kamar an zuba ruwa na a kwando domin ko a daren Juma’ a sai da maharan suka far wa kauyen Dan-Dambo inda suka jidi abinci sannan su tarwatsa mutanen garin da har aka ruwaito cewa sun yi lalata da wasu daga cikin matan da suka taras a kauyen.

Share.

game da Author