PDP ta daba wa kanta wuka ne zaban Ashiru da sauran ‘yan takara da ta yi a Kaduna – Sani Bello

0

Darektan shirye-shirye na kamfen din dan takarar gwamnan jihar Kaduna a jam’iyyar APC kuma gwamnan jihar Nasir El-Rufai, Sani Bello ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ta daba wa kanta wuka ne a dalilin ‘yan takaran da suka tsayar.

Sani Bello ya ce PDP ta tsayar da yan takara ne da basu cancanta ba.

Sani Bello ya bayyana haka ne a taron magoya bayan jam’iyyar APC a filin wasa na Ranchers Bees dake Kaduna.

” Ina kira a gare ku mutanen jihar Kaduna da kada ku ma yi asarar kuri’un ku wajen zaben jam’iyyar PDP, domin basu tsayar da ‘yan takarar da suka cancanta ba. Ku fito kwan ku da kwarkwatan ku ku zabi Nasir El-Rufai a zarce a ci gaba da kwankwadan romon Dimokradiyya.

A yau Laraba ne jam’iyyar APC a jihar Kaduna ta kaddamar da kamfen din ta domin fafatawa a zaben 2019.

A wannan taro jam’iyyar ta mika wa wadanda suka lashe zabukan fidda gwani tuta.

Share.

game da Author