Nine na cancanci zama kakakin jam’iyyar APC ba Lanre Issa-Onilu ba – Abubakar Usman

0

Wanda ya zo na biyu a zaben kujerar kakakin jam’iyyar APC, Abubakar Usman ya shigar da kara kotu yana neman ta da ta dakatar da kakakin jam’iyyar APC Lanre Issa-Onilu cewa ba shi ya kamata jam’iyyar ta nada kakakin ta ba tunda shine ya zo na hudu a zaben.

Usman ya na neman kotu ta tilasta wa jam’iyyar ta sauke Lanre ta nada shi tunda shine ya zo na biyu a zaben.

” Babu yadda za a ace wanda ya zo na hudu a kujerar da zabe ake yi a nada shi kakakin jam’iyyar mu, APC. Kamata yayi a lokacin da Bolaji Abdullahi ya ajiye aikin sa, sai a nada wanda ya zo na biyu a zaben. Kuma nine na zo na biyu a zabe.” Inji Usman.

Usman ya shigar da karar ne domin a bi masa hakkin sa a yi abin da doka ta shimfida.

” Ko a dokar jam’iyyar da na hukumar zabe da na kasa ma gaba daya babu inda aka ce yadda aka yi ne daidai sai dai kuma idan an canja tsarin ne. Amma dokar da na sani har yanzu abin da aka yi saba mata ne.

Share.

game da Author