Dabi’un mu ne suke wahalar damu. Mata ku daina cewa babu miji, firgita samarin kuka yi suka daina zuwa zance wajenku, albishirin ku, suna can buhu-buhu a gidan kallon ball saboda auren ku yayi musu tsada, gwara su rage dare a can tunda kun ce dole sai mai kudi, dole kowa ya sha wahala, shi babu mata, ke kuma babu miji.
Kun taba ganin an haifi mutum da dukiya? Kuma abun mamaki, iyayen yanzu da abokai suna taka rawar gani wajen saka wa ‘ya’yansu da abokansu buri a zuciya.
Daga zarar ‘yar su ta yi saurayi talaka sai a kyaleta da shi, kowa sai ya juya mata baya a gidansu shiyasa samari suke shiga rigar masu kudi saboda talauci kashe musu kasuwa yake. Gaskiya, ba a gane cikakken matsayin mutum daga nesa.
Matasa ku kwantar da hankalinku, karya da buri basa canza wa mutum rayuwa. Allah ne yake canza maka rayuwa idan yaso. A tunani na, babu kwanciyar hankali ga namijin da ya dogara da arzikin matarsa, a zance na gaskiya ma, abu daya ne babu laifi idan matarka ta fika, shine kyau, wanda zai zamo maka hujjar rufe mata baki idan tayi maka gori.
Misali, za ta iya ce maka ta fika kyau, kai kuma sai kace mata: Kalleki duk kyan ki kin qare a aurena ni mummuna. Bana jin za ta sake magana.
Saidai abun mamaki sai a samu ‘dan talaka ko ‘yar talaka suna soyayya ko zaman aure amma suna gani kamar alfarma suke yiwa junansu. To da irin wa kuke buri ku aura? Ku manta da abun da kuke gani a wasan hausa a matsayin rayuwar aure. Wannan ai ‘drama’ ce, don a fim din hausa ne za ka ga anyi aure yau, gobe kuma an nuno amarya da ango akan qaton ‘dining table’ suna cin kaza, ga babban gida da mota. To idan haka ne sai draktan fim din ya nuna muku lokacin da angon yake cikin fatara kafin yayi kudi.
Buri ne ya haifar da karya a cikin duniyar matasa, shiyasa makaryata suka yi yawa yanzu sai kuma aure yayi wahala. Don ko a dandalin sada zumunta ba a gane talaka tunda da wuya ka samu saurayi ko budurwa suna bayyana cikakken matsayinsu a rayuwa. Nasan za ku yi mamaki irin yadda yanzu auren jari yayi yawa, da yawa daga cikin samari sun daina ganin darajar ‘ya’yan talakawa.
Sai dai abun mamaki shine shima auren jarin ba irin na da bane, suma attajiran sun zama na karshen duniya, ba a morarsu don an auri ‘ya’yansu, da wuya ka ga maikudi ya bawa ‘dan talaka ‘yar sa saidai ko mai rauni ce ko kuma ta kafirce masa. Har gwara ya kyaleta ta kai shekara 40 idan bata samu irin wanda yake so ba. Kaje gidajen wasu masu kudin ka sha mamaki.
Ahirr dinku ‘yan mata, ku tsaya a matsayinku. Kada ki sake qawa ta zigaki ta raba ki da saurayinki saboda hassada tunda ba lalle bane ita tana da irin sa saidai karya da buri kamar ita zata yiwa kanta ba Allah ba. Duk gudun talaucinku bu ku kai maikudi gudunsa ba.
Yadda kuke burin auren ‘dan maikudi ko ‘yar maikudi shima haka maikudi yakeso ya aurawa ‘yarsa ko ‘dansa ‘ya’yan masu kudin da suka fishi kudi. Ku yi soyayya don Allah sai ku zauna lafiya. Allah ne yake kwantar da hankalin mutane idan suka yi masa biyayya.
Allah ya shiryar damu.