NEMAN BELI: Dasuki ya ce a dakatar da shari’ar sa har sai gwamnati ta bayar da belin sa

0

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dage sauraron shari’ar tsohon Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara a Fannin Tsaro, Sambo Dasuki.

Ta dage sauraren karar har zuwa 9 Ga Janairu, 2019.

Hakan ya faru ne bayan da Dasuki ya nemi jin dalilin da za a ci gaba da tsare shi, alhali ba sau daya ba, ba sau biyu ba kotu na umartar gwamnatin tarayya a sake shi, amma gwamnatin ta na bijire wa umarnin kotu.

Mai Shari’a a Babbar Kotun, Ahmed Mohammed ne ya dage karar jiya Talata, bayan da lauyan mai shari’a ya shigar da korafin cewa bai ga dalilin da zai sa lauyan mai kara, wato lauyan gwamnatin tarayya ya ci gaba sa gurfanar da Dasuki ba, domin ita ma gwamnatin ta bijire wa umarnin kotu.

Lauyan Dasuki ya ce a dakatar da shari’ar har sai ranar da gwamnatin Najeriya ta bi umarnin kotu na ranar 2 Ga Yuli, inda kotu ta umarci gwamnati ta bada belin Dasuki da gaggawa.

Dama a baya Dasuki ya ce ba zai sake halartar kotu ba, har sai bayan an bayar da belin sa, sannan zai rika halarta daga gida.

Shi da Antoni Janar kuma Ministan Shari’a Abubakar Malami, ya ce gwamnati ba za ta saki Dasuki ba saboda wasu dalilai da suka shafi kasa.

Share.

game da Author